Hoto: Shugaba Tinubu tare da shugabannin kungiyoyin ma’aikata
Manyan ƙungiyoyin ƙwadago biyu a Najeriya, wato Nigeria Labour Congress da kuma Trade Union Congress sun sanar da dakatar da yajin aikin da suka fara yi a ranar Litinin.
Ƙungiyoyin biyu sun sanar da wannan mataki ne bayan kammala tattaunawar shugabannin ƙungiyoyin biyu yau Talata, a Abuja.
Ƙungiyoyin ƙwadagon sun tsunduma yajin aiki ne bayan gaza cimma matsaya tsakaninsu da gwamnatin tarayya kan abin da zai zama albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata a Najeriya.
Jim kaɗan bayan kammala taron, ƙungiyoyin ƙwadagon sun ce sun janye yajin aikin ne domin hanzarta tattaunawar da ake yi tsakanin su da gwamnati game da albashi mafi ƙanƙanta, wanda shi ne babban abin da ya janyo taƙaddamar.
Zaman da shugabannin NLC da TUC suka yi a ranar ta Talata ya mayar da hankali ne kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyoyin da gwamnatin a wata ganawa da suka yi ranar Talata tare da sakataren gwamnatin tarayya.
Yajin aikin dai ya taɓa ɓangarori daban-daban na tattalin arziƙin Najeriya, ɗaya daga ciki shi ne katsewar lantarki a faɗin ƙasar.
A cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, NLC ta ce “an dakatar da yajin aikin na mako ɗaya domin kammala tattaunawa.”
Tun farko, a ranar Talata ƙungiyar ta bayyana cewa za ta ci gaba da yajin aikin har sai shugabannin ƙungiyar sun kammala tattaunawa kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyar da gwamnati.
Yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnati
A ranar Litinin ne gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Litinin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar, George Akume a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin sai abinda hali ya yi da kungiyoyin kwadagon suka fara a wannan rana.
Bangarorin biyu sun shafe sa’oi biyar zuwa shidda suna tattaunawa da juna kuma a karshe sun cimma matsaya a kan wasu batutuwa.
Ministan yada labaran kasar Mohammed Idris ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta amince ta yi kari a kan naira dubu 60 wanda shi ne sabon albashin mafi karanci na ma’aikata da ta gabatar wa kungiyoyin kwadagon tun farko, wanda suka yi fatali da shi.
Ministan ya yi ikirarin cewa a karkashin yarjejeniyar da suka cimma kungiyoyin kwadagon sun amince su janye yakin aiki:
“Na farko za su janye wannan yajin aiki nasu, na biyu kuma gwamnati ta yi alkawarin za ta sake duba mafi karancin albashi da ake biyan ma’aikata, watau naira dubu 60 domin ayi mu su kari”.
”Na uku za a ci gaba da tattaunawa tsakaninmu da ‘yan kwadago, kwamiti da gwamnati ta kafa zai ci gaba da tattaunawa da su na kusan sati daya, kusan kullum za su yi ta ganawa domin a samu sabon tsari na mafi karancin albashin da za a rika biyan ma’aikata” in ji shi.
A dayan bangaren kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun ce za su gudanar taron Majalisar koli a ranar Talata da safe domin su tattauna kan matsayar da suka cimma da jami’an gwamnati.
Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya Komrade Kabiru Ado Minjibir ya shaidawa BBC cewa an baiwa kwamitin da aka dorawa alhakin tsara sabon albashi mafi karanci kwanaki bakwai ya kamala tattaunawa da kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki wajan tsayar da mafi karancin albashi:
”A bangarenmu mun yi alkawarin za mu kira taro na Majalisar koli wanda ya hada da wadannan kungiyoyi na NLC da TUC domin a tattauna sannan a fidda matsaya,” in ji shi.
Game da maganar wutar lantarki kuwa, kungiyar kwadago ta NLC ta ce majalisar dokokin kasar ta ce ta yi wani kuduri da ya nemi a mayarda farashin kudin lantarki kamar yadda yake a baya.
Comrade Minjibir ya ce ‘yan Majalisar dokokin kasar sun yi alkaurin za su ci gaba da bibiya domin su tabbaar cewa wannan umurni nasu, majalisar zartarwa ta yi amfani da shi.
Ga alama a wannan karo ƙungiyoyi da dama sun yi biyayya ga umarnin ƙungiyar ƙwadagon wajen shiga yajin aikin.
Cikin ƙungiyoyin da suka shiga yajin aikin sun haɗa da:
Ƙungiyar ma’aikatan jiragen ƙasa ta Najeriya
Ƙungiyar ma’aikatan lantarki ta ƙasa
Ƙungiyar likitoci da masu aikin lafiya ta Najeriya
Ƙungiyar ƴanjarida ta Najeriya
Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da gasa ta Najeriya
Ƙungiyar ma’aikatan ɓangaren shari’a ta Najeriya
Gamayyar ƙungiyoyin ma’aikatun hukumomin gwamnati
Ƙungiyar ƙwararrun ma’aikatan harkokin jiragen sama ta Najeriya
Ƙungiyar injiniyoyin gine-gine da masu haɗa kayan ɗaki ta Najeriya.