Gwamnati Ta Yi Alƙawarin Biyan Bashin Albashin Ma’aikatan Lafiya Kafin Ƙarshen Watan Agusta

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya cewa za ta biya bashin albashin watanni bakwai da suke bi kafin ƙarshen watan Agusta 2025. Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate, ne ya bayyana haka a wani taron haɗin gwiwa da shugabannin manyan ƙungiyoyin ma’aikatan lafiya a Abuja.

Wannan mataki ya biyo bayan wa’adin kwanaki 21 da ƙungiyar likitoci ta ƙasa (NMA) ta bai wa gwamnati don magance matsalolin walwala, tare da barazanar yin yajin aiki na ƙasa.

A baya-bayan nan, ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta ƙasa (NANNM) ta dakatar da yajin aikin gargadi bayan shiga tsakani daga masu ruwa da tsaki. Don kauce wa sake samun cikas a fannin kiwon lafiya, ma’aikatar lafiya ta shirya babban taro na musamman da ya haɗa da NMA, NANNM, da ƙungiyar hadin gwiwar ma’aikatan lafiya (JOHESU), tare da wakilai daga Ma’aikatar Harkokin Jin Kai.

Bayan taron, Farfesa Pate ya jaddada kudirin gwamnati na biyan bashin albashin da suke bi, tare da nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirye don magance matsalolin da suke kewaye da tsarin kiwon lafiya a ƙasar. Shugaban NMA, Farfesa Bala Audu, da shugaban JOHESU na ƙasa, Kwamared Kabiru Minjibir, sun bayyana fatan cewa gwamnati za ta cika alkawuranta, domin hakan zai iya hana faruwar yajin aikin da ke tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *