Wasiyya 10 daga Marigayi Sheikh Ɗahiru Bauchi

A daidai lokacin da ake ci gaba da ta’aziyya da jajen rasuwar fitaccen Malamin addinin musulunci, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, har yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan rayuwa da rasuwar malamin.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 shahararren malamin ya rasu a wani asibiti da ke Bauchi.

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar marigayin, ciki har da Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima da gwamnoni da sarakuna da sauran mutane, har da ƙasashen waje.

Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne ya jagoranci yi wa malamin sallah a masallacin Idi na garin Bauchi kafin a binne shi a masallacinsa da ke garin da misalin ƙarfe 6:45, kuma an binne shi ne kusa da wasu daga cikin iyalansa da suka rasu a baya.

Sheikh Ɗahiru wanda jagora ne na ɗarikar Tijjaniyya ya rasu yana da shekaru 98 a kalandar miladiyya, a kalandar Musulunci kuma ya haura shekara 100 da ƴan watanni.

Ɗansa, Naziru Ɗahiru Bauchi ya ce mahaifinsa gajeriyar rashin lafiya ya yi, duk da dai a baya ya kan yi fama da rashin lafiya saboda yawan shekaru.

‘Ya daɗe da shirya mutuwa’
Domin jin irin wasiyoyin da malamin ya yi ga al’ummar duniya, BBC ta tuntuɓi ɗaya daga cikin ƴaƴan shehin malamin, Dr. Abubakar Surumbai Sheikh Ɗahiru, wanda ya ce yawanci malamin ya bayyana wasiyoyinsa ne a cikin karatuttukansa da ya yi a zamanin rayuwarsa.

Ya ce, “muna miƙa ta’aziyyarmu zuwa ga al’ummar Musulmin duniya baki ɗaya da ma Kirista saboda kowa akwai irin amfanin da ya yi masa, musamman wajen haɗin kan ƙasa da kare haƙƙin ƴan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya. Ta’aziyya ce ta kowa da kowa ba ƴaƴa da matansa kaɗai ba,” in ji Surumbai.

Sai dai ya ce a maganar wasiyya, mahaifin nasu ya kasance mutum ne na kowa, da yake isar da saƙonnin ta’aziyyarsa ga kowa.

“Shi rayuwarsa ta ƙare ne a ibada da shiryar da bayin Allah. Don haka a cikin karatunsa ne za mu fahimci wasiyoyinsa, da kuma irin wasiyoyin da yake yawan faɗa,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa marigayin ya daɗe yana wa’azi tare da kira ga mutane da su yi riƙo da Alqur’ani da riƙo da addini.

Surumbai ya ce shehin malamin ya daɗe yana bayyana shirinsa na mutuwa, tare da kira da a haɗa kai a zauna lafiya. “Yana cewa ya riga ya ɗaura kayansa, an kai masa tasha, abin da ya sa bai tafi ba, shi ne motar ce ba ta cika ba, kuma da zarar ta cika za a kira shi kuma zai tafi,” in ji shi.

Wasiyya
Game da irin wasiyoyin shehin malamin, Dr Surumbai ya ce akwai wasu wasiyoyin da suka san malamin yana yawan faɗa a zamanin rayuwarsa, inda ya lissafa wasu daga ciki:

Yana yawan wasiyya da tsoron Allah
Wasiyya da riƙo da Qur’ani: Yana yawan wasiyya da karatun Qur’ani da tilawa
Yin abu don Allah
Rashin kwaɗayi: Ka da mu raga ko mu tauye wani abu saboda abin duniya
Riƙo da ɗarikar Tijjaniya
Riƙo da wazifa
Tabbatar da haɗin kanmu ƴaƴansa baki ɗaya
Tabbatar da haɗin kai tsakaninmu da almajiransa
Tabbatar da haɗin kan Musulmin duniya baki ɗaya ko da kuwa akwai saɓani
Ka da a haɗa ni da manyan shehunnai – “Ni ba komai ba ne”, inji Sheikh a wata murya da ke yawo.
Ya ƙara cewa a lokuta da dama, yana yawan maganar karatun Qur’ani. “Ko hutu na dawo a lokacin da nake karatu, yana yawan tuna min cewa in riƙe Qur’ani, in dage da tilawa,” in ji Dr Surumbai.

Me Shehu ke nufi da ya ce ka da a yi masa mauludi?

Akwai wani sautin murya da aka riƙa yaɗawa a kwanakin baya, inda a ciki aka ji muryar da aka ce ta Sheikh Ɗahiru Bauchi ce yana cewa bai ce a shirya manyan tarukan maulidinsa ba don gudun ka da a haɗa shi da manyan magabata, lamarin da Surumbai ya ce tawalu’u ne irin na marigayin.

“Ai wannan tawalu’u ne . Ai ko Shehu Ibrahim (RTA) ba shi ya roƙa a riƙa yi masa maulidi ba. Irin abin nan da Hausawa suke cewa yaba kyauta tukuici, ba wanda zai ba ka abu ba ne zai ce ka yi masa wani abu, idan ya yi haka, ya zama kasuwanci ke nan,” in ji shi.

Sai dai ya ce ana yin maulidi domin tunawa tare da yaba aikin alheri da wani bawan Allah ya yi.

“Don haka idan mutum ya maka abun alheri, ba shi ne zai ce ga abu kaza da za ka saka maka ba da shi ba, kai ne za ka yi abun da kake ganin zai ji daɗi, ya san cewa ka san ya maka abun alheri.”

A ƙarshe ya ce irin darussan da suka koya daga rayuwar malamin suna da matuƙar muhimmanci, waɗanda ya ce matuƙar aka yi riƙo da su, za a zauna lafiya kuma za a samu kwanciyar hankali.

“Muna godiya ga Allah da rayuwarsa da tsayin da ta yi da ma karantarwarsa. Muna roƙon Allah ya ba mu ƙarfin gwiwar haɗin kai da ƙoƙarin tsayawa tare da ci gaba da gudanar da ayyukan da ya bari.”

Mun kwafo daga shafin BBC Hausa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *