Shugaba Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (ritaya), a matsayin Ministan Tsaro na ƙasar, a wani taro da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis.

Rantsarwar ta biyo bayan murabus ɗin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar a ranar 1 ga Disamba, wanda ya buƙaci a sauke shi daga muƙamin saboda dalilan lafiya. A ranar Talata ne aka sanar da sabon suna, aka tura wa Majalisar Dattawa, wadda ta yi gaggawar tantancewa da amincewa da shi.

Janar Musa, wanda aka haifa a Sokoto a 1967, ya shiga aikin soja a 1991 bayan kammala horo a matsayin ƙaramin laftanar. Ya yi dogon aiki a rundunar, inda a 2023 Shugaba Tinubu ya naɗa shi Babban Hafsan Tsaro, kafin ya yi ritaya a watan Oktoba 2025.

A lokacin da yake jagorantar rundunar tsaro, Janar Musa ya yi fice wajen ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sassan tsaro domin inganta ayyukan yaki da rashin tsaro.

Da aka rantsar da shi a yau, zai fara aiki nan take, yayin da Gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin ƙarfafa nasarorin tsaro da aka samu baya-bayan nan da kuma hanzarta sauye-sauyen da ake gudanarwa don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin ƙasar.

A wajen rantsarwar akwai Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Jagoran Majalisar Dattawa Opeyemi Bamidele, Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar Dattawa Sanata Adeniyi Adegbonmire, Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, da Mai Ba da Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.

Matar sabon ministan, Mrs Lilian Oghogho Musa, Babban Hafsan Tsaro Janar Olufemi Oluyede, Bishop Matthew Hassan Kukah na Cocin Katolika ta Sokoto, da Justice Kumai Bayang Akaahs (ritaya) suma sun halarci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *