Abin da ya sa Ridha Clinic ya zama inuwar kowa

Daga Muhammad Idrees

Cikin burin wannan Harka akwai samar da wasu abubuwa da za su amfani al’umma da rage musu radadin yanayi da kuma koyar da su yadda ake gudanar da wadannan abubuwan.

A gaba-gaba na kan wannan buri, akwai abu biyu, samar da makarantu na gaske, tun daga Firamare, Sakandare da ma Jami’o’i, sai kuma samar da asibitoci ingantattu.

A kan hakan da’irori da dama na ta yunkuri, a wasu wuraren an iya samar da makarantu zuwa matakin Sakandare ko da dai ba su kai ingancin da ita Harka din ke so ba, kamar yadda muka sha ji a bakin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).

A ta bangaren samar da asibiti kuwa ba na jin akwai inda aka samar sai dai kokarin ’yan’uwa na ISMA a garuruwa daban-daban da ba ya buya.

Bayan kammala karatun a wani mataki ya samar da wajen ba da magani, kama-kama har abu ya bunkasa zuwa ginannen asibiti da ake kira Ridha Clinic a garin Gombe.

Ibrahim Abdulkareem matashi ne ba mai shekaru ba da ya taso da son aikin lafiya a rayuwarsa tun yana karami, hakan ya sa ya karkata karatunsa ta bangaren lafiya.

Tun kusan shekara guda na ji labarin asibitin, don haka na kuduri aniyar sai na je na gane wa idona, domin ina son jin ci gaba irin wannan.

Tun a kan hanya na rika lura da wucewar marasa lafiya da masu jinya dauke da ‘flas’ na shayi. Ina zuwa farfajiyar asibitin na ga mutane jingim, maza, mata da yara, kai har da tsofaffi, wasu na wash! Wasu ana sannu!!

Ban yarda na shiga asbitin ba sai da na nemi jin ta bakin wasu cikin marasa lafiya, amma na yi rashin sa’a na fara da wata Bafillatana da ko Hausa ba ta ji da na ga ta kawo ’yarta. Nan dai muka yi maganar kurame ni da ita, tunda ni ban jin Fulfulde, ita kuma ba Hausa. Nan na yi mata Allah ya sawwake.

Hira ta biyu da na yi ita ce, wata Hajiya ce da ta kawo ’yarta. Ta shaida min ba su fi rabin awa ba suka kawo ta ranga-ranga, amma cikin ikon Allah ga ta da sauki. Don na samu tana wasa ne a lokacin.

Hakan ya kara min kaimin bin mutane da dama, kuma kowa yabo yake da sam barka. Zan tsakuro muku hirarrakin na ban mamaki da karfafa gwiwa nan gaba.

Kofar shiga asibitin za ta kai ka wani falo wajen karbar kati, wanda na tarar da wata matashiya na ta faman shigar da wasu bayanai a wani katon littafi, bayanta da kantoci cike da fayil-fayil na marasa lafiya, gefe guda da ababen zama na masu jiran ganin Likita bayan an kira sunansu. Can gaba na lura da wata siririyar hanya mai kofofi a gefen hagu da dama wanda tun kan na je na ayyana dakunan kwantar da marasa lafiya ne.

Daga karshen kuma akwai dakin gwaje-gwaje (laboratory) da na tarar da ma’aikata ana ta faman gwaje-gwaje wanda su ma na yi hira da wasu daga cikinsu.

Akwai kuma wani babban daki a gefe kusa da wajen ba da magani, shi wannan dakin yana da gadaje fiye da ragowar dakunan, shi ma na zanta da wasu marasa lafiyar da masu jinya. Na lura a dakin ba da magani mai aikin guda daya ce, kuma kamar an mata yawa, haka dai sama-sama na ji ta bakinta na wuce ina ba masu karbar magani hakuri.

Wani abu da na lura shi ne, irin haba-haba da ma’aikatan asbitin ke yi wa marasa lafiya da kuma tsaftar asibitin duk da irin cinkoson da asibitin ke fama da shi.

Bayan kare wannan zagaye nawa ne na bukaci a sada ni da shi mai wannan asibiti, wanda a lokacin ma da marasa lafiya na jiransa. Kafin ya samu sukuni ya sallami wanda yake gani sai na lura kusa da ni da wata mata da kamar ba mara lafiya ba, kuma da alamun ’yar’uwa ce Ahlus Sunna, don haka na matsa na tambaye ta ko ta kawo wani ne?

Ta ce min a’a, kanta ta kawo. Na nemi jin me ya same ta? Maimakon ba ni amsa kai tsaye, sai ta dakko min tarihi. Ta ce min ta taba yin hadari a mota aka kai su asibitin gwamnati amma Wallahi kusan awansu guda ba a zo an duba su ba, daga nan wani dan’uwanta ya dakko ta ya kawo ta nan, ana zuwa nan da nan ma’aikata suka zo kanta aka kai ta gado Likita ya zo ya duba ta aka mata wata allura. Ta ce min; “A takaice dai a daren ta fara samun saukin duk wani zogi da nake ji. To tun daga ranar na daina zuwa kowane asibiti ni da iyalina, sai nan.

“Nan za a mutuntaka, a kula da kai, ba kyara ko kadan. Sannan ga sauki na kudi a komai. Kai hatta magani Wallahi sai ka je kasuwa ka ji sun fi nan tsada, dole ka dawo nan din…,” in ji ta,

Karar budewar kofar ofishin Likita ta katse hirarmu. Ina daga kai aka ce min Bismillah. Na ce Malama na gode, zan shiga ganin Likita ni ma.

Shiga ta ofishin Likita na lura da kyau da tsarin ofishin, ofishi ne irin na kowane asibitin kudi da ka sani mai dauke da komai da komai da ya kamata.

Cikin fara’a Likita ya min barka da zuwa, ya nuna min kujera na zauna. Idan a waje aka ce wa wannan bawan Allah din da ke gabana shi ya samar da wannan asibiti yake kuma gudanar da shi, zai wahala ka aminta. Matashi ne mai fara’a da kunya, mai zuciya cike da himma da tausayi.

Ibrahim Abdulkareem haifaffen Jihar Gombe ne, ya samu sha’awar aikin lafiya tun yana yaro a wani zuwa asibiti da mahaifiyarsa ta yi da shi. Hakan ya sa bayan kare makarantar Sakandare ya karkata zuwa ga karatun lafiya.

Yadda aka fara har wannan asbiti ya samu shi ne kowa zai so ji. Ya shaida min cewa ya fara ne da karamin dakin ba da magani (chemist), inda kama-kama abu ya rika bunkasa har ta kai da dole ya fara tunanin samar da asibitin sukutum duk kuwa da matsaloli da kullen da za a fuskanta.

Wannan aniya ta sa shi bin duka hanyoyin da suka dace na Hukuma har aka samu takardar yarjewa, sannan ya yunkura don ganin an samar da muhalli wanda shi ne yanzu asibitin yake.

Sunan wannan asibiti bai buyar wa kowa ba, don kuwa suna ne na daya daga cikin Limaman Shiriya. Ya shaida min tun lokacin da Malam (H) ya yi wani bayani dangane da Imam Ridha (AS) kan neman lafiya da samun waraka, wanda har su Malam (H) suka kawo labarin wani Bature da dansa mara lafiya, wanda yaron ya samu sauki ya yanke shawarar yin tawassuli da wannan suna ga yunkurinsa na samar da lafiya cikin wannan al’umma. Wannan kuma shi ne sirrin wannan asibiti da duk nasarorin da aka samu.

Mal. Ibrahim ya shaida min cewa suna matukar ganin tasirin wannan tawassuli a ayyukansu, domin sau tari za a kawo mara lafiya bayan an kai shi wasu asibitocin wanda za ka ga akwai cutukan da dole jinyarsu iri daya ce, amma sai a zo nan mu maimaita abin da aka yi wa mara lafiya a wani wuri bai warke ba, cikin ikon Allah, sai kawai ya samu sauki a nan wurinmu. Wannan ba zai kirgu ba.

Da na tambayi nasarori kuwa, sai Abdulkarim ya ce; “Alhamdulillah. Ana gudanar da asibitin nan ne ta kowane bangare cikin nasara. Tun daga ma’aikata zuwa kayan aiki. Wuta ba ta yankewa, ana dauke NEPA muke kunna janareto. Sannan babbar nasara ita ce waraka da mutane kan samu a zuwan su wannan asibiti namu, ta yadda har mamakin irin sikkar da suka samu da mu muke yi. Sau tari, kamar yadda kowa ya sani, harkar lafiya akwai na sama, idan aka zo da wani yanayi da ya fi karfinmu mukan tura zuwa gaba (referral), amma sai mara lafiya ya dage ya nace cewa shi lallai a nan zai zauna. Ko mun nuna hadarin hakan, sai su dage. Wani ma sai ka ji ya ce ko rasuwa zai yi, to shi ya fi so ya yi a nan!

“Haka nan saboda karancin wuri, za ka ga mun nuna a yi hakuri a je wani asibitin ga mutum a wani yanayi na damuwa, amma sai ya dage cewa shi ko saman daki ne don Allah a kai katifa a kwantar da shi, ba damuwa, maimakon ya tafi! To irin wannan suna da yawa. Don haka kullum muna yi wa Allah godiya.

“Babbar matsalar da muke fama da ita kuwa ba ta wuce ta karancin muhalli ba. Dakunan kwantar da marasa lafiya sun yi kadan. Sannan hatta wajen karbar marasa lafiyar da farfajiyar duka sun yi kadan. Wannan kusan ita ce matsalarmu a yanzu,” in ji shi.

Haka dai muka yi sallama, don masu son ganin sa sun kagu. Ina fitowa wata mai nikabi ta ce min; “Amma kun dade Wallahi.” Na ce a yi hakuri!

Ban bar asibitin nan ba sai da na kara jin ta bakin wasu daga cikin ma’aikatan, inda kusan dukkansu suka yi ittifaki wajen kirki, tausayi da mutuntaka ta mai gidansu.

Sun fada min ta dalilin dabi’unsa ya sa su ma duk suke koyi. Akwai wadda ta ce min za ka ga an kawo mutum ba lafiya, ba kudi, wani lokacin ko na gwaji babu, amma haka zai zo ya ce a yi, ba komai.

Na lura da wani mai shayi a gefen asibitin wanda masu jinya kan je don karyawa, na san za a samu labarai. To kuma lallai na ji da dama tun daga irin aminci da kulawar da marasa lafiyar ke samu ta bakin masu jinya da kuma sam barka da sukan yi wa wannan bawan Allah mai wannan asibiti.

Ya ce min; “Ka ga wannan bawan Allah din, Wallahi sai dai kawai a ce Allah ya saka masa da alheri. Kullum sai na ji sabon labari wajen bakin masu jinya da masu yi masu rakiya. Kai akwai fa wani da ya zo aka kwantar da shi ba kudin da zai iya biyan aikin da aka masa, amma a hakan kuma mai asibitin nan ya sayo shinkafa da kayan cefane ya sa aka aika gidan mutumin nan!”

Wannan duka a takaice ne, mai bukatar cikakken bayani ya nemi rahoton bidiyo da muka yi don gane wa idonsa.

Babban darasin dai a duk wannan rahotanni shi ne, nuna wa ’yan’uwa yadda wannan bawan Allah shi kadai ya iya samar da asibiti sukutum yake gudanar da shi, ya kuma cimma nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *