Abokina da ya gargaɗe ni kan saka jari a Najeriya, yanzu yana min dariya in ji Dangote

Hamshaƙin mai kuɗin nan, Alh. Aliko Dangote ya bara, yana mai cewa: “Shekaru huɗu da suka wuce, wani abokina mai kuɗi ya fara kwashe kuɗinsa yana mayarwa a ƙasashen waje. A lokacin na yi adawa da wannan mataki nasa, na kuma roƙe shi da ya sake tunanin matakin da ya ɗauka domin maslahar ƙasarsa da kishin ƙasarsa.

“A lokacin shi abokin nawa ya yi ƙorafin cewa, akwai rashin daidaiton manufofi a siyasar Najeriya, ga kuma cin hanci da rashawa, wanda hakan ya hana shi sanya kuɗinsa a kasuwancin Najeriya.

“Sai ga shi kuwa yana mani dariya a cikin ‘yan kwanakin nan, yana cewa dama ya gargaɗe ni, kuma ga abin da ya yi mani fargaba nan ya fara tabbata” in ji Dangote.

Alhaji Dangote yana wannan bayanin ne ganin yadda gwamnatin Tinubu ta hana sabon kamfanin matatar man fetur da ya gina samun mai daga Nijeriya da kuma sai da shi a Nijeriyar.

Wannan al’amarin da ɗaure kai yake ganin cewa, kamfanin nan a Nijeriya yake, a Lagos, ɗanyen man fetur ɗin nan ma a Nijeria ake hako shi, masu buƙatar man nan yawancinsu a Nijeriya suke, amma saboda wasu masu riƙe da madafun iko suna amfana da tsarin siyo tataccen man daga waje, sun ki sakar wa kamfanin Dangote mara. Sun kuma hana Kamfanonin tace man ma na gwamnati da ke cikin ƙasar su yi aiki tsawon shekara da shekaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *