Allah Ya yiwa shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Danzago rasuwa.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Aminiya ta ruwaito, Marigayi Alhaji Ahmadu Haruna ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya kuma daya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ya tabbatar da rasuwar marigayin a asibiti.
A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 ne dai Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nada Alhaji Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaban hukumar REMASAB.