Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jajanta wa gwamnati da al’ummar Jihar Borno sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Mallam Abubakar Nakwada, Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, ta wakilci gwamnan a Maiduguri.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa maƙasudin ziyarar ita ce jajanta wa Gwamnatin Borno da al’ummar jihar kan ambaliyar ruwa mai ratsa zuciya.
Yayin da yake miƙa saƙon jaje na Gwamna Lawal a fadar gwamnatin jihar Borno, Mallam Abubakar Nakwada ya sanar da gudunmawar Naira Miliyan 100 da gwamnatin jihar Zamfara ta bayar a matsayin nuna goyon baya da tallafawa.
Ya ce, “A madadin jama’a da gwamnatin jihar Zamfara, ina rubutu domin nuna alhininmu game da mummunar ambaliyar ruwa da ta afku sakamakon ballewar ruwa daga madatsar ruwa ta Alu da ke Maiduguri.
“Muna matuƙar baƙin ciki da rahotannin da ke cewa sama da mutum miliyan ɗaya ne suka rasa muhallansu sakamakon wannan ibtila’i.
“Lamarin wannan ibtila’i yana ratsa zuciya. Al’ummar jihar Zamfara – waɗanda suka fuskanci irin wannan ibtila’i, duk da cewa bai kai na Borno ba – suna yi wa ‘yan uwansu maza da mata a yankunan abin ya shafa addu’ar ‘Allah Ya mayar da alkhairi, Ya kuma kiyaye faruwar hakan a nan gaba’, yayin da suke cikin wannan mawuyacin hali. Muna roƙon Allah Ta’ala ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu, ya kuma mayar wa waɗanda suka rasa dukiyoyinsu da mafificin alkhairi.
“A matsayin nuna goyon baya da tallafawa, gwamnatin jihar Zamfara na bayar da gudunmawar zunzurutun kuɗi Naira Miliyan 100,000 domin gudanar da ayyukan agaji da kuma taimaka wa al’ummomin da abin ya shafa a Maiduguri.
“Muna roƙon Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ci gaba da taimakon waɗanda abin ya shafa, ya ba su ƙarfin gwiwa da juriya wajen sake gina rayuwarsu.