‘An rufe idona tare da daure ni tsawon kwanaki 45″: Bafalasdinen da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta saki

Wani Bafalasdine wanda yana daya daga cikin ‘yan kurkuku da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta saki a ranar Asabar a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta ya bayyana irin halin gallazawa da ya samu kansa a hannun kasar ta mamaya.

Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na kafar watsa labaru ta Press TV, Ibrahim Mohammad Khaleel al-Shawish ya bayyana cewa a tsawon kwanaki 45, an “rufe ma shi ido, daure shi da tursasashi ya zukunna kasa” kafin a canza mashi wuri zuwa kurkukun Negev ta Haramtacciyar Kasar Isra’ila inda ya fuskanci “shocking” na wutar lantarki da hare-hare na karnuka.”

Shawish ya fito ne daga Hanoun da ke arewacin Gaza kuma an kama shi ne a ranar 10 ga watan Disambar 2023. Fuskarsa a fili ta nuna alamun rashin abinci da horo.

Yayin da ya ke bayyana irin halin da fuskanta a barikokin Haramtacciyar Kasar Isra’ila inda aka ajiye shi ya ce “Abu ne wanda ba za a iya bayyana shi ba,” Shawish ya ce, “Duk wani nau’in horo akwai shi a can. Za su iya yin amfani da “shocking” na wutar lantarki a kan ka, kuma ana amfani da “shocking” na wutar lantarki a wurin horo. Bayan haka ana amfani da karkuna a wurin horo.”

“Al-Kassam Brigades” wanda shine reshen soji na kungiyar fafutikar Falasdinawa ta Hamas, a ranar Asabar ta mika wadanda ta yi garkuwa da su ‘yan Haramtacciyar Kasar Isra’ila zuwa hannun kungiyar bayar da agaji ta kasa-da-kasa (ICRC) a birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza.

Haramtacciyar Kasar Isra’ila, a nata bangaren, ta sako Falasdinawa daga kurkuku su 183 a matsayin bangare na biyar na musayar fursunoni a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *