An yaba wa Daliba da Malamai na Makaratar Fudiyya a Mairuwa Jihar Katsina

Daga Awwal Jibril ‘Yankara
A ranar Asabar 6-1-2024 ne ‘Yan Uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky NA Da’irar Mairuwa da ke karamar Hukumar Faskari Jihar, Katsana.
Suka gudanar da Taron bikin Yayen Dalibai wadan da suka Kammala Saukar Alkur’ani Maigirma.
Taro Wanda ya gudana A harabar makarantar ya samu halartar Dinbin Al-Umma so sai.
An gabatar da Jawabai masu ratsa ji so sai masu ratsa jiki Domin riko da Alkurani Babban Bako a Wuri Shi ne Shaikh Abdulhamid Bello Zariya.


A nasa Sakon Injiniya Samaila Mu’azu Bawa Faskari Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar hukumar Faskari jihar Katsina Wanda ya sami Wakilcin Mataimaikin sa na Musamman Malam Nurideen Adamu Kanon haki
Ya yaba wa Dalibai da Malamai na Makarantar kuma ya yi kira ga Daliban da su daure suyi koyi da koyarwar alkuranin kamar yada aka koyar da su, Domin samun Tsira Duniya da Lahira inji Shi
Har walayau Danmajalisar ya baiwa makaratar kyautar Tsabar kudi Naira Dubu Ashirin da sukara wajen gudanarwar makarantar, Yakuma yabawa Malaman So sai kuma yace Yana tare dasu Dari bisa dari
Shi ma anasa sakon Jawabin General manager of katsina state housing authority, HON Engr Aminu Barau Mairua,
Wanda ya sami Wakilci Malam Bello Barau
Ya yaba Ma Namijin kokarin da Malaman Makarantar Suke yi waje Bayar da tarbiya, ya ce ba abin da Za a ce masu illah Allah saka masu da Mafificin Alkhairi
Sannan Ya ba Makarantar Gudumuwar Naira Dubu Hamsin da ci gaba da gudanar da Makarantar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *