Ba bambanci tsakanin Netanyahu na Isra’ila da Hitler – Tayyip Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, a ranar Laraba ya ayyana Isra’ila a matsayin “kasar ta’addanci” wadda shugabannin ta “dole a hukunta su a kotunan kasa-da-kasa.” Kamar ya ke a cikin wani rahoto na kafar watsa labarai ta Sahara Reporters

A cewar Reuters, Erdogan ya ma bayyana cewa babu wani banbanci a tsakanin Firaministan kasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da Adolf Hitler, wani shugaba da aka yi a kasar Jamus mai nuna karfin iko kan mutane a tsakanin shekarar 1933 har zuwa lokacin da ya kashe kansa a shekarar 1945. Hitler ya fara yakin duniya na biyu a nahiyar turai ta hanyar afkawa kasar Poland a shekarar 1939 kuma yana da ruwa da tsaki a kisan Holocaust, kisan Yahudawa kimanin miliyan shida da sauran wa]anda hakan ta shafa da aka yi.

Shugaban na Turkiyya ya kamanta hare-haren Isra’ila a Gaza da halin da Yahudawa suka samu kan su a hannun Nazi.

A rahoton na Reuters, Erdogan ya jaddada cewa kasashen yamma da ke goyon bayan Isra’ila suna da hannu a cikin aikata laifuffukan yaki.

“Suna magana mara dadi a kan Hitler. Menene banbancin ku da Hitler? Za su sa mu rinka tunanin Hitler. Shin abinda wannan Netanyahun ke yi yayi wani banbanci da abinda Hitler ya yi? Ba banbanci.” A cewar shugaban na Turkiyya.

“Ya fi Hitler dukiya, yana samun goyon baya daga kasashen yamma. Duk wani kalar taimako yana zuwa daga kasar Amurka. Kuma me suke yi da duk wannan taimakon? Sun kashe sama da mutane 20,000 da ke Gaza.” Kamar yadda ya bayyana.

Sai dai a cikin martaninsa, Netanyahu ya ce shugaban kasar Turkiyya ne na karshe da ya kamata ya koya wa Isra’ila wani abu.

“Erdogan wanda ya yi kisan kare dangi kan Kurdawa, wanda ke da tarihin kulle ‘yan jarida a kurkuku wa]anda ba su goyon bayan mulkinsa, ” Netanyahu ya bayyana a cikin wani jawabi, “Shi ne mutum na karshe da zai yi mana wa’azin halayya Mai kyau.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *