Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya biya sama da Naira Biliyan Biyar na kuɗaɗen ma’aikatan da suka ritaya da aka riƙe musu sama da shekaru 13.
Tun a watan Fabrairun bana ne Gwamnatin Jihar Zamfara ta fara biyan ma’aikatan jihar da Ƙananan Hukumomin da suka yi ritaya kuɗaɗen giratuti bayan an tantance su.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta biya Naira 5,347,243,210.00 ga waɗanda suka yi ritaya daga Jihar da kuma Ƙananan Hukumomi.
Sanarwar ta ce, an biya ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da malaman firamare 2,209 da suka yi ritaya, yayin da ma’aikatan jihar 1,642 da suka yi ritaya aka biya su a kashi biyar.
“Ma’aikatan jihar su 4,198 da suka yi ritaya suna bin bashin jimlar Naira 8,095,948,906.63.
“Rukunin farko, na biyu, na uku, da na huɗu na 1,382 daga cikin 4,198 da aka tantance ’yan fansho na jihar, an biya su jimillar haƙƙoƙinsu wanda ya kai N2,336,271,961.37 daga cikin N 8,095,948,906.63 da suke bi.
“A kwanan nan an biya kashi na biyar na ’yan fansho na jiha 260 bashin giratuti na Naira 510,094,956.35.
Hakazalika, an biya ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da malaman firamare 465 da suka yi ritaya jimillar kuɗi Naira 500,969,762.47 a karo na biyar.
“A ɗaya ɓangaren kuma, ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da malaman firamare 2,209 da suka yi ritaya an biya su kashi biyar da suka kai Naira 2,500,876,293.16. Waɗanda suka ci gajiyar biyan kuɗaɗen su ne waɗanda suka yi ritaya daga shekarar 2012 zuwa 2019.”