A ciki gaba da gudanar da bukukuwan cika shekara ɗaya a karagar mulkin jihar Zamfara, ranar Litinin ne Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da wasu manyan ayyuka guda biyu a Ƙananan Hukumomin Bakura da Maradun da ke yankin Zamfara ta Yamma.
Ƙaddamarwar na ɗaya daga cikin manyan ayyukan da Gwamnatin Dauda Lawal ta aiwatar cikin shekara guda.
A wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa gwamnan ya ziyarci ƙananan hukumomi uku: Mafara, Bakura, da Maradun.
Ya ƙara da cewa, a ƙaramar hukumar Talatan Mafara, gwamna Lawal ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda ya sami babban asibitin ƙaramar hukumar Talata Mafara a lalace.
“A yau, a ci gaba da ƙaddamar da wasu ayyuka da aka kammala a shekarar farko da Gwamna Lawal ya yi kan mulki, Gwamnan tare da rakiyar tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, sun ƙaddamar da sabuwar Kwalejin Noma da Fasaha da aka gyara a garin Bakura.”
A jawabinsa wajen ƙaddamar da kwalejin, Gwamna Lawal ya ce; sama da shekaru ashirin da kafa Kwalejin Noma ta Bakura, tsarinta ya lalace, inda ba za a iya koyo ko koyarwa a muhallin ba.
“A matsayinmu na gwamnatin da ta bayyana ilimi da noma a cikin manyan abubuwan da ta sa a gaba, mun ga ya dace a gyara kwalejin tare da adana mata muhimman abubuwan da za a samar da ingantaccen ilimin aikin gona.
“Mun kuma ɗaga darajar Cibiyar daga Kwalejin Noma da Kimiyyar Dabbobi zuwa Kwalejin Noma da Fasaha ta Bakura. Hikimar da ke tattare da wannan ita ce baiwa kwalejin damar gabatar da wasu fasahohi a matsayin abin da ake buƙata don sauye-sauyen ɗaga fasahar zamani a kwalejin.
“Saboda haka, a yau mun taru a nan domin ƙaddamar da ayyukan gyare-gyaren da aka gudanar a kwalejin. Waɗannan sun haɗa da gyara ɓangaren masu gudanarwa, ɗakin gwaje-gwajen iri da sauran abubuwan da suka shafi noma, ɗakin gwaje-gwajen ƙwayoyin halitta, ɗakin gwaje-gwajen abubuwan da suka shafi kimiyya, babban ɗakin lakca da ɗakunan kwanan ɗalibai. Har ila yau, an gina wasu bankunan manyan baƙi guda biyar tare da inganta tsarin ruwa na kwalejin.”
Yayin da yake a ƙaramar hukumar Maradun, Gwamna Lawal ya yi dubi da yadda ake gudanar da aikin gyaran babban asibitin Maradun.
“Kwangilar aikin ta haɗa da gyaran ɓangaren masu gudanarwa, ɗakunan majiyyata maza da mata, ɗakunan kwana na ma’aikata, ɗakin ajiyar gawa, babban ɗakin tiyata, da banɗakuna guda biyu. Sauran ayyukan sun haɗa da katange asibitin, samar da isasshen ruwa na asibitin, hanyoyin tafiya da kayan aiki gaba ɗaya.”
A ƙaramar hukumar Talatan Mafara, gwamna Lawal ya nuna rashin gamsuwa da rashin jin daɗin sa a kan halin da babban asibitin Talatan Mafara yake, inda nan take ya bada umarnin gyara da inganta shi.
“Akwai matuƙar tada hankali ganin halin da babban asibitin Talatan Mafara ke ciki. Ba zan lamunci irin halin da na ga asibiti a ciki ba a lokacin bincike na. Abin da ke nuni da yadda ’yan siyasarmu ke karkatar da dukiyar ƙasa, waɗanda galibi suke aiwatar da al’amura marasa muhimmanci.
“Na bada umarnin gyara da inganta asibitin nan take. Za mu samar da kayan aikin asibitin don samar da gyara da kuma zama babban jigo ga sauran cibiyoyin kiwon lafiya a yammacin jihar. Inganta yanayin sa zai samar da tsayayyen kiwon lafiya a yankin.