Bitar kundin yadda Yahudawa suka tsara mallake duniya

 

TARE DA YUSUF KABIR

Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu holds a cabinet meeting in Jerusalem November 13, 2019. REUTERS/Ronen Zvulun

An tarjama littafin zuwa harshen Nasara, an kuma sanya masa suna “The Zionist Plan for the Middle East” ko kuma “A Strategy for Israel in the Nineteen Eighties.” Farfesa Isra’iil Shahak ne ya tarjama shi.

Ga ]an bayani a kansa: Isra’ila Shahak Farfesa ne a fannin ilimin kimiyyar halitta a Jami’ar Hebrew a Kudus, kuma shugaban }ungiyar Isra’ila ta “Human and Civil

Rights”. Ya buga The Shahak Papers, matattarar manyan labarai daga jaridar Hebrew press, kuma shi ne marubucin labarai da littattafai masu yawa, daga cikin su akwai Wanda ba Bayahude ba a }asar Yahudu (Non-Jew in the Jewish State). Littafinsa na baya-bayan nan shi ne Rawar Isra’ila na duniya: Makamai don Danniya (Israel’s Global Role: Weapons for Repression), wanda AAUG ya buga a cikin 1982. Israel Shahak:

(1933-2001)

Jagoran Harkar Musulunci Shaikh Ibraheem Zakzaky (h) ya yi bayanin wannan mugun shiri da Yahudawa suka yi domin mallake duniya yana mai cewa: “Hankoron su ba Palestine bane ka]ai, za su kafa daula ce ta haramtacciyar }asar sahayina da za ta mamaye dukkanin wannan yankin, wanda ya ha]a da }asashen Falasɗinu da Urdun da Syria da Labanon da Arewacin }asar da ake cewa Saudi Arabia, har da Birnin Madinah. Sun zana taswira wadda suka shigar da Madina a ciki. Su a wajensu za su mamaye wannan wurin ne, su tunaninsu kenan. Insha Allahu wannan mafarki nasu ba zai ta~a yiwuwa ba, amma kuma duk da mafarki ne suna ta ta’asar su; saboda haka ya kamata duk Musulmi su nuna damuwarsu.”(SZakzaky Office 1/11/2023).

A laburare na wata katafariyar Jami’a, tun shekaru 3 baya na sha cin karo da jibga-jibgan littafan da aka rubuta dangane da Yahudawa, Palas]inu da ta’addancin da suka yi, da kuma makircinsu ga Duniya. Manyan marubuta da Duniya ta san da zamansu, littafansu suka zamanto madogara ga ]alibai a Jami’oin duniya; sun yi rubuce-rubuce masu tarin yawa a kan hakan. Masanan diflomasiyya, masu bincike na tarihi da masanan tsaro matu}ar suna da tausayi, dole su tausaya wa Palas]inu da yin tir da Yahudawan da suke da a}idar Sahyuniyanci.

Littafin “The Protocols of the elders of Zion,” littafi ne da Yahudawa suka zauna suka tsara yadda za su mamaye duniya ta hanyoyi mabambanta, ta yadda sai abin da suka ce a yi sannan za a yi.

Kimanin sati 6 bincike ya kai ni ga wannan littafi da yanzu haka yana nan a intanet. Duk wanda ya bincika zai sami PDF ]insa na Larabci da Turanci. Na karanta na Larabci da Turancinsa. Na Larabcin fitaccen marubuci Mansur AbdulHakeem ne ya tarjama shi. Ga abin da ya kawo a yayin tarjamarsa: “Sanin abu da ankarewa da shi, aiki da basira da tunani }arfi ne wanda Yahudawa ke kawar da duk wanda yake amfani da su domin aiwatar da rayuwarsa. Hakan ya sa suke ya}ar duk wanda ya karanta littafin ko kuma yake ya]a shi.”

Fitaccen marubuci ]an }asar Misra da littafansa ake dogaro da su wajen yin digiri na 1,2,3 a kai; shi ne Abbas Mahmoud Akkad. Wannan fitaccen marubucin ya yi bincike tattare da tabbatar da maganar tsare-tsaren Yahudu domin mallake duniya.

Littafi ne da ya yi bayanin irin tsare-tsaren sirrin yadda Yahudawa za su mulki duniya ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban. Waɗannan hanyoyin sun haɗa da dabarun tattalin arzi}i, haifar da }iyayya tsakanin mutanen duniya, amfani da bambancen addinai, a}idodi da mazhabobi, ya}e-ya}e, yaɗa labaran }arya ta hanyar amfani da kafafen yaɗa labaru, shagaltar da mutane daga barin abubuwa masu matu}ar girma na gina rayuwa, zuwa shagaltuwa da wa}e-wa}e da kaɗe-kaɗe, wasanni, haifar da kokwanto cikin zukatan masu addinai da sauransu.

A cikin littafin sun bayyana cewa: “ Ha}i}a za mu nutsar da duniya cikin mayatar wasannin motsa jiki, har sai an wayi gari }asashe da al’ummomi ba su shagala da manyan abubuwa, sai dai kawai za su koma kula da }ananan ababe, su yi sabo da su ta hanyar da za su kasance kamar jini a jiki gare su. Sai su manta manyan muhimman abubuwan ci gaban rayuwa saboda sabonsu da shagaltuwarsu da }ananan ababen da suka ɗauke hankalinsu.

MURADAI 5 DA HANYOYIN DA ZA SU CIM MASU

 1. Zabar matsoratan shuwagabanni.

Sharhi: Ga duk wanda ya kalli shuwagabannin na mafi rinjayen }asashe, zai ga cewa babu abin da suka fi tsoro kamar Amurka, Isra’ila da Faransa. Wa]annan sune iyayengidansu da suke tsoro.

 1. Samar da rarraba a tsakanin mutane.

Sharhi: Tabbas matu}ar al’umma tana da hain kai, ba za a yi galaba a kan ta ba. A yayin da kuwa ta rasa ha]in kai, to babu abin da za ta tsinana mai amfani a duniya ballantana na lahira. Duk wata rarraba a tsakanin Musulmi ta fannin Shi’a/Sunna, to Yahudawa ne suka samar da ita, su suke gudanar da ita a zahiri ko ba]ini. Duk wata rarraba da ke tsakanin Ahlus Sunna, Yahudawa ne suka haifar da ita. Bugu da }ari duk wata rarraba da ke tsakanin Shi’a, to Yahudawa ne suka haifar da ita. Duk wata rarraba da ke cikin }ungiyoyi, to tabbas Yahudawa ne suka samar da hakan, ta hanyar samar da ma’aikatansu a zahiri ko ba]ini.

 1. Rusa mutuncin Malaman addini.

Sharhi: Malamai suna da matu}ar daraja, kuma su ne ginshi}an al’umma. A duk sad ka ga wa]ansu mutane na aibanta da sukar Malamin da yake kira zuwa ga ha]in kai, yake amfanar da al’umma ba tare da bambancin addini ko a}ida ba, to tabbas aikin Yahudawa ne kai tsaye. Na tuna sad da Saddam Husaini ya sanya aka rubuta littafin ‘Lillah thumma littarikh’ domin ~ata Imam Khumaini (qs) da juyin Musulunci. Wannan ma misali ne.

 1. Mallake kafafen ya]a labarai:

Sharhi: Kafafen ya]a labarai da su ake juya duniya a da da yanzu. Da su Mu’awiya ya yi amfani wajen bayyana wa Shamawa cewa, Imam Ali (as) ba Musulmi ba ne. Da su ne aka yi amfani wajen wanke Fasi}i Yazeedu (LA) da bayyana Imam Husaini (as) a matsayin mai ja da Gwamnati. Yahudawa sun bayyana cewa, za su mallaki jaridu, mujallu, marubuta da Gidajen Talabijin ta hanyar sayen Editoci da Daraktocin Media ]in da ma}udan ku]a]e masu gusar da hankali.

 1. Amfani da mata.

Sharhi: Mata sun kasance wa]anda ma}iya a shekaraniya, jiya, yau da gobe ke amfani da su domin yin galaba a kan ma}iyi. Yahudawa sun kasance wa]anda suke aurar da yaransu mata kyawawa ga shuwagabannin }asashen Larabawa da kuma ma duk wanda suke so su juya shi. Galiban Sarakunan Larabawa suna da ala}a da matan banza wa]anda sun haifi ‘ya’ya da su, wasu ma sun aure su. Idan ka bi tarihi a jiya da yau za ka riski hakan.

Wa]annan nu}u]o]in ka]an ne daga abin da wannan littafin da muka ambata ya }unsa.

GIRGIZAR AQSA DA MAKOMAR SIYASAR NATANYAHU

Akwai mabambanta ra’ayoyi dangane da Ambaliyar A}sa da ya faru a 7 ga watan Oktoba dangane da yaye-zani-a-kasuwa da rundunar Hamas ta yi wa Haramtacciyar }asar Isra’ila da ake ganin tana ]aya daga cikin }asashe mafi }arfin tsaro a gabas ta tsakiya.

Manazarta, masanan tsaro, da fitattun ‘yan Jarida sun ri}a bayyana yadda wannan kayen da Hamas ta yi wa Isra’ila a matsayin abin kunyar da ba zai ta~a goguwa ba, zai ri}a bin ta har }arshenta.

Jaridu da daman gaske a birnin Tel-aviv na Haramtaciyyar }asar Isra’ila sun wallafa wannan shan kayen da hukumar Banjamin Natanhayahu ta sha. Duk da a gefe guda, Isra’ila ta kashe mutane dubbai (musamman }ananan yara da mata), ta kuma rushe ]aruruwan gine-gine, ta lalata kadarorin Miliyoyi, amma tozarcin da aka mata shi ne mafi muni a tarihinta tun sad da aka haifar da }asar shekaru 70 baya.

A wata mu}ala da Hayem Lipison ya rubuta, wacce jaridar Harritace ta wallafa a Isra’ila cewa: “Tabbas Ambaliyar Aqsa ba aikin zubar da jini ba ne ba kawai, a’a lamari ne na yaye-zani a kasuwa da Hamas ta aiwatar.” Jaridar ta wallafa hotunan }wararrun Sojin Isra’ila sanye da kaki, dakarun Hamas sun kama su. Da ganin haka, duk abin da Isra’ila za ta yi kawai lamari ne na borin kunya, amma ba zai ta~a haifar mata da ]a mai ido ba.

Marubucin ya ci gaba da cewa, tabbas mun kar~i shan kaye. Tabbas an yi galaba a kanmu. Wannan nasarar ta Hamas ya faru ne a zamanance da kuma wayewar da Isra’ila ba ta samu hakan ba. Cikin sau}i ba tare da ~ata lokaci ba, Hamas suka sami damar ya]a ya}in nan cikin biranen Isra’ila. Tabbas zamantakewar Isra’ila da rayuwar }asar ba zai ta~a dawowa kafin 7 ga watan Oktoba ba.

 1. Shaida ta biyu ita ce wani fitaccen marubuci mai suna Jadoon Lipy ya yi rubutu a dai ita wannan jaridar, inda ya ambata cewa: “{asar nan tamu (HKI) ta ga wa]ansu hotuna wa]anda ba ta ta~a tsammanin za ta gan su ba a rayuwarta, domin hakan kuwa dole Hukumar }asar ta aiwatar da wani ya}i a kan Gazza domin mayar da martani, amma kuma ba za ta ta~a farfa]owa daga wannan naushin da Hamas ta yi mata ba har abada.”

Ya ci gaba da cewa, tabbas ]aruruwan maya}an Palas]inawa sun tabbatar da cewa, ba zai ta~a yiwuwa a takura rayuwar miliyoyin al’ummarsu ba tare da sun ]auki fansa ba. Sun keto katangar da ita ce mafi tsaro da kyamarori, sun keta ko’ina tattare da kwashe abubuwan amfani da sirrikanta. Wani abin kunya shi ne, sun }aryata batun cewa, Isra’ila ta san tsaro, kuma za ta iya kare wata }asar. Mutane yanzu za su fahimci ita kanta ta kasa kare kanta, ta wace hanyar za ta kare wasu?”

Palas]inawa a Gazza sun tabbatar da cewa, suna shirye da bayar da dukkanin abin da ke hannunsu domin }watar ‘yancinsu. A yayin da ]an jaridar ya tambayi Lipy shin Isra’ila za ta ]auki darasi daga abin nan da ya faru kuwa?” Sai ya ce: “A’a, babu tabbacin samun hakan.”

Da daman fitattun marubuta a haramtacciyar }asar Isra’ila, suna ganin tallafin da Amurka da }awayenta ke kai wa Isra’ila, ba zai iya }watar }asar daga Hamas da sauran rundunonin fafutikar samar da ‘yancin Palas]inu ba. A wani ~angaren kuma matsa lambar amfani da miyagun makamai wajen kashe }ananan yara da kai hari Asibitoci, zai haifar da mummunan yanayi a yankin, domin kuwa kowace }asa (musamman masu adawa da a}idar Sahayuniyanci) za ta shirya kasancewa a fagen ya}i.

Wannan ne ha}i}anin al’amari, kuma duk wani mataki da Isra’ila za ta ]auka a yanzu; to ta aiwatar da shi shekaru 30 baya, kuma babu abin da ya }ara wa Palas]inawa sai sadaukarwa da marmarin bayar da rai.

RA’AYOYIN MASANAN TSARO DA SIYASA A KAN MAKOMAR NATANYAHU DA SIYASARSA

A nan kuma za mu bayyana ra’ayoyin wasu daga cikin ‘yan HKI dangane da makomar Natanyahu. Kamar yadda labarai a ranar 16/10/2023 suka rawaito cewa, bayan harin 7 ga Oktoba na Ambaliyar A}sa, makomar siyasar Natanyahu zai kasance cikin tsanani da rashin tabbas. Hakan kuma na komawa da yadda aka kashe manyan jiga-jigan rundunar da ake bayyana ta da ba za a ta~a galaba a kan su ba. Ga wasu daga cikin ra’ayoyin:-

 1. Daniel Simon, }wararren ne a fagen siyasar Isra’ila, sannan yana cikin manyan masananta a }asar. Ya bayyana cewa: “Tabbas ‘Ambaliyar Aqsa’ da Hamas suka aiwatar shi ne alamun farko na rushewar }asar Isra’ila.” Duk da ba wannan ne farkon alamomin da aka gani ba dangane da }arshen mulkin Natanyahu ba, sai dai wannan ya fi muni da }azancewa.
 2. Bugu da kari a wata hira da Simon ya yi da wakilin wata Jarida a Faransa, ya bayyana cewa: “Natanyahu ya kasa cika al}awarin da ya ]aukarwa talakawansa na kare su, don haka zai kar~i farashi mai tsada dangane da hakan.”
 3. Shi kuma Hanan Kiristal, mazanarci a kan siyasar Isra’ila, ya bayyana wawancin Natanyahu a yayin da ya bayyana cewa: “Natanyahu bai bin dokokin Gwamnati, yana kuma yi musu karan-tsaye. A yanayin nan da ake ciki, mutanen Isra’ila ba su da wani za~i illa fantsama tituna domin aiwatar da zanga-zanga a kan abubuwan da suke faruwa.”
 4. A yayin da Elder ya bayyana cewa: “Natanyahu ya gaza ta kowane fage, domin kuwa hatta tawayen da yake fuskanta daga Kwamandojin Soji bai kula da lamarin. Ya kafe da raina cewa, Hamas ba za ta iya shige masa hanci da }udundune ba.”
 5. Shi kuma Micheal Bin’amiy, shugaban Kotun warware matsalolin jama’a, ya bayyana cewa: “Dama akwai Hukuma guda ]aya da take tsara rayuwar }asa da mutanenta, tun da Natanyahu ba ya sauraron mu, lallai zai kar~i farashin hakan.”

 

 

 

An gabatar da gagarumin bikin mi}a satifiket na darajojin shuhadah a Malumfashi

Kwamitin Ahl-Duthour, ha]in gwiwa da Mu’assatus Shuhadah na yankin Katsina da kewaye, sun gabatar da bikin mi}a satifiket ga wa]anda suka shiga sahu da nufin samun darajoji don samun ceton Shahidai ta hanyar yankar DARAJOJIN SHUHADAH a yankin Malumfashi da kewaye.

Bikin ya gudana ne a ranar Talata 19/12/2023 a harabar makarantar Fudiyya Malumfashi. Kuma ya }ayatar sosai-sosai, saboda ya sami halartar ’yan’uwa daga kowane sashe na yankin Malumfashi, Kafur, Rigoji da sauran su.

An }arfafa ‘yan’uwa sosai a kan taimakon Iyalan Shahidai ta hanyar yankar wa]annan DARAJOJIN SHUHADAH a wannan shekara.

An bayar da satifiket ga wa]anda suka shiga sahu a shekarar da ta gabata 2022, an kuma }addamar da shirin bana 2023. An sami mahalarta da yawan gaske sun yanki fom na bana.

An kuma ba da kyauta ta musamman ga yankin Malumfashi da kewaye a matsayin wa]anda suka yi zarra a taimakon Iyalan Shahidai na babin Yankan DARAJOJIN SHUHADAH a wannan shekara.

Malam Kabir Imam Malumfashi da Mallam Ashiru Rigoji ne suka karbi wannan babbar kyauta da Mu’assatus Shuhadah ta tanada ga wannan yankin daga babban ba}o mai jawabi a bikin, Shaikh Yakubu Yahya Katsina, wanda ya gabatar da dogon jawabin }arfafa mahalarta a wannan taro.

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *