Bayan ya yi sanadiyyar rasuwar dubunnan mutane da tayar da miliyan 12 daga muhallansu, yakin Sudan ya jefa yankuna biyar na kasar cikin yunwa, kamar yadda The New Arab ta ruwaito.
Sai dai kamar yadda kafar watsa labarun ta bayyana, a karon farko a kusan shekaru biyu na yaki, dakunan dafa abinci da ake dafa miya a kasar Sudan da ke fama da yunwa an tilasta dole su cewa mutane su tafi biyo bayan dakatar da agaji da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi ga hukumomin da ke ceton rayuwar.
“Mutane za su rasu sakamakon wannan matakin.” Kamar yadda wani dan sa kai mai tattara kudade na Sudan wanda ke kokarin tattara kudi domin ciyar da dubunnan mutane a babban birnin kasar Khartoum ya bayyana.
“Muna da dakunan dafa abinci 40 a fadin kasar da ke ciyar da mutane tsakanin 30,000 zuwa 35,000 a kullum.” Kamar yadda wata ‘yar sa kai ta Sudan ta shaidawa AFP, inda ta shaida cewa duka an kulle su biyo bayan sanarwar Trump cewa ya dakatar da bayar da taimako zuwa kasashen waje da kuma wargaza hukumar agajin kasa-da-kasa ta Amurka (USAID).
“Mata da yara ana cewa su tafi domin ba za mu iya yi masu alkawarin za mu ciyar da su ba kuma.” Kamar yadda ta bayyana, inda ta nemi da kada a bayyane sunanta domin yin magana ga al’umma na iya haifar da matsala ga aikinta.
Kasar Sudan ta fada cikin yaki ne tun watan Afirilun shekarar 2023, kuma a mafi yawan kasar dakunan dafa abinci da ke samar da miya wanda al’ummu ke kula da su ne kawai hanyar da ta hana jama’a da dama fadawa cikin yunwa kuma da yawansu sun dogara ne da kudaden da Amurka ke samarwa.
“Wannan matakin na janye samar da kudade nan take na na da sakamakon da zai iya kawo karshen rayuwa.” Javid Abdelmoneim, shugaban kungiyar likitoci ta “Doctors Without Border (MSF)” ya shaidawa AFP a birnin Omdurman.
“Wannan kuma wani bala’i ne ga mutanen Sudan wadanda tuni suke fama da sakamakon yaki, yunwa da lalacewar tsarin lafiya da taimakon kasa-da-kasa wanda bai kai yadda ake bukata ba.” Kamar yadda ya kara da cewa.
Amurka itace kasar da ta kawo taimako wanda ya fi yawa a Sudan a shekarar da ta gabata, inda ta samar da dalar Amurka miliyan 800 ko kashi 46 cikin 100 na shirin aikin da majalisar dinkin duniya ta ke yi.
A yanzu haka majalisar dinkin duniya ta yi kididdigar cewa tana da kasa da kashi 6 cikin 100 na kudaden da ta ke bukata domin aikin agaji a Sudan a shekarar 2025.
Sama da mutane miliyan 8 na gaf da fadawa yunwa a Sudan, kamar yadda “Integrated Food Security Phase Classification” da ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya ta bayyana.
Ana sa ran yunwa ta yadu zuwa karin akalla yankuna biyar na Sudan zuwa watan Mayu, kafin damina mai zuwa da ke da yiwuwar sa kaiwa ga abinci ya zama mafi wahala a fadin kasar.