Halima Ibrahim, daluba da ke aji biyu na babbar sakandaren kimiyya da fasaha ta ‘yan mata da ke Potiskum, ta rasu a ranar Alhamis bayan fadowar da ginin makarantarsu ya yi suna tsakar daukar darasi.
Kamar yadda PM News ta ruwaito, wasu daluban hudu a yanzu haka suna samun kulawar likita sakamakon mummunan al’amarin .
Dakta Bukar Aji, sakataren dindindin na ma’aikatar ilimin kasa da sakandare da babbar sakandare ta jihar Yobe, ya tabbatar da faruwar al’amarin yayin taron manema labaru a ranar Alhamis a Damaturu.
Ya bayyana cewa al’amarin ya faru ne da misalin karfe 1 na rana a ranar Alhamis inda ginin aji mai kashi biyu ya rushe a kan dalubai suna tsaka da daukar darasi.
“A hakikanin gaskiya, abinda ya faru, gini ne, mai ajujuwa guda biyu, ya fado a gurin wucewa mai tsawo na ajin.
“Cikin rashin sa’a, daluban mu biyar abin ya shafe su.
“Daya daga cikinsu ta rasu biyo bayan hakan, hudu suna a cikin yanayi mai kyau, kamar yadda likitan da ke asibiti ya bayyana.” Kamar yadda Aji ya shaida.
Sakataren na dindindin ya ce akwai akalla dalubai 50 a cikin ajujuwan, inda kowanne ke dauke da dalubai 25.
“Suna a cikin aji ne kuma daluban aji 2 ne na babbar sakandare.
“Mun ziyarce su kuma a hakikanin gaskiya sun tsorata.” A cewar Aji.
Sakataren na dindindin ya bayyana cewa yana jiran rahoton musamman ne daga makarantar domin su sanar da ma’aikatar gidaje halin da ake ciki.
“Ma’aikatar na da kwarewa na gano musabbabin matsalar tare da gano matakan da za a iya hana faruwar hakan a nan gaba.” Kamar yadda ya bayyana.