Dole ne mu daina barin bambancin addini da ƙabilanci yana raba kan mu a matsayin mu na ‘yan ƙasa, inji Ministan Yaɗa Labarai

Wata tabbatacciyar hanya ta samun haɗin kan ‘yan Nijeriya wadda ba ta bari bambancin ƙabilanci, addini, da siyasa ya raba kan mu ba ita ce ta samar da wani labari mai ban sha’awa na ƙasa, mai ƙarfafa amana da amincewa a tsakanin ‘yan Nijeriya, inji Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai.

Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai ga ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, shi ne ya ruwaito hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, inda ya ce Idris yana jawabi ne a wajen taron farko na Masu Magana da Yawu wanda Cibiyar Hulɗa Da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta shirya tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta Tarayya a ranar Talata a Abuja.

Da yake jawabi kan taken taron, wato “Canza Labari, Canza Al’umma”, ministan ya ce bisa la’akari da bambance-bambancen da Nijeriya take da shi, akwai buƙatar a samar da haɗin kan ƙasa wanda ya zarce ƙabilanci, addini, da siyasa ta hanyar ƙirƙiro da labari mai ban sha’awa na ƙasa, wanda ke ƙarfafa amana da amincewa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Ya ce babban gangamin wayar da kan jama’a na ma’aikatar sa mai taken “Kundin Tsarin Ɗabi’un Nijeriya” wanda nan ba da daɗewa ba Shugaban Ƙasa zai ƙaddamar da shi, ya ƙunshi yarjejeniyar zamantakewa tsakanin ƙasar da ‘yan ƙasar, kuma zai kasance wani shiri na tsarin ɗabi’un ƙasa wanda ke bayyana ‘yan Nijeriya da kuma ƙarfafa halayen su a matsayin su na ’yan ƙasa.

Idris ya ce, “Abu na musamman game da wannan Kundin Ɗabi’un shi ne yarjejeniya ce ta zamantakewa tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa kuma tana ɗauke da Manyan Wajibai Bakwai na ƙasar Nijeriya ga ‘yan ƙasa da kuma Alƙawura Bakwai na ‘yan ƙasa ga da ƙasar su. Jigon Kundin Ɗabi’un shi ne dole ne gwamnatin da zaɓaɓɓu da naɗaɗɗun wakilai ke wakilta ta cika wasu muhimman alƙawura don samun muhimman alƙawura daga ‘yan ƙasa.”

Haka kuma ya yi tsokaci kan amana a matsayin ginshiƙin hanyar sadarwa mai inganci kuma mai ɗorewa, yana mai cewa yayin da makomar sadarwa ke nuni ga fasaha, fasahar za ta iya yin tasiri mai ma’ana ne kawai idan aka ɗora ta kan amana.

Ya ce: “Amana ta kasance muhimmin abu wajen gina dangantaka; na kai, na ƙungiya, har ma da na al’umma.

“A matsayin mu na masu magana da yawu, muna buƙatar mu yi ƙoƙari na gaske don gina amana da maido da fata tagari a duk inda muke. Dole ne ginawa da kiyaye amana ya zama wani nauyi da ya rataya a wuyan kowa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *