Falasdinawa 31,819 aka kashe, 73,934 suka jikkata a Gaza – Ma’aikatar lafiya

Akalla Falasdinawa 31,819 aka kashe kuma 73,934 suka jikkata tun 7 ga watan Oktoba sakamakon yakin Isra’ila a zirin Gaza, kamar yadda ma’aikatar lafiya a zirin ta bayyana a ranar Talata.

Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, Falasdinawa 93 aka kashe kuma 142 suka jikkata a cikin awowi 24 da suka gabata, kamar yadda ma’aikatar ta kara da cewa.

A wani bangaren, kafar watsa labarun ta ruwaito cewa majalisar dinkin duniya ta ce hana agaji kaiwa ga Gaza da Isra’ila ke yi na iya zama laifin yaki.

“Matakin cigaba da hana agaji shiga Gaza da Isra’ila ke yi, tare da yadda ta ke cigaba da hare-harenta, na iya zama yin amfani da yunwa a matsayin wani salon yaki, wanda laifin yaki ne.” Kamar yadda babban kwamishinan hakkin dan Adam na majalisar dinkin duniya, Volker Turk, ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *