Falasdinawa 369 za su fito daga kurkukun Haramtacciyar Kasar Isra’ila a ranar Asabar

Haramtacciyar Kasar Isra’ila za ta sako Falasdinawa 369 da ke tsare a kurkukun ta a ranar Asabar a karkashin musayar fursunoni kashi na shida a Gaza, kamar yadda The New Arab ta ruwaito kungiyar da ke fafutika ta Falasdinawa ‘yan kurkuku ta shaida a ranar Juma’a, bayan da rikici a yarjejeniyar ya kusa jefa Gaza cikin yaki.

Kungiyar mai fafutika ta Falasdinawa ‘yan kurkuku ta bayyana cewa Haramtacciyar Kasar Isra’ila “za ta saki mutane 36 ‘yan kurkuku da aka yankewa hukuncin-rai-da-rai a kurkuku” domin harin da suka yi kan ‘yan HKI, inda ake sa ran za a fitar da 24 daga cikinsu kasar waje, da kuma Falasdinawa 333 da aka kama aka tsare a yayin yakin.

Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta bayyana cewa ta karbi sunayen mutane uku da aka yi garkuwa da su domin musayarsu da Falasdinawan.

HKI ta bayyana cewa ‘yan HKI din da za a saki din sune dan HKI da ke Amurka Sagui Dekel-Chen, dan HKI da ke Rasha Sasha Trupanov da dan HKI da ke Agentina Yair Horn, kamar yadda ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu ya bayyana.

Wadanda za a saki din mayakan Gaza ne ke ruke da su tun bayan harin 7 ga watan Oktobar 2023 a kan HKI.

HKI ta yi gargadi ga Hamas cewa sai ta sako wadanda ta yi garkuwa da su masu rai mutum uku a karshen makon nan ko kuma yaki ya dawo, bayan da kungiyar ta ce za ta dakatar da sakin nasu kan abinda ta kira karya yarjejeniyar da HKI ta yi.

Yarjejeniyar wadda ta fara a ranar 19 ga watan Janairu ta kasance ta samu matsala biyo bayan shawarar shugaban kasar Amurka Donald Trump na mallake yankin, inda mutanen da ke zirin Gaza sama da miliyan biyu za su koma Misra ko Jordan.

Kasashen Larabawa sun hadu wajen yin watsi da shirin, kuma Saudi Arabiya za ta karbi bakuncin shugabannin Misra, Jordan, Katar da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a ranar Alhamis domin yin taro kan al’amarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *