Gidauniyar Aig-Imoukhuede ta ƙaddamar da kamfen don Sauya Cibiyoyin Kula da Lafiya na Farko a Najeriya

Gidauniyar Aig-Imoukhuede, wata babbar ƙungiya mai zaman kanta da ta himmatu wajen inganta ayyukan yi wa jama’a hidima a nahiyar Afirka, ta sanar da wani kamfen na farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya na farko (PHCs) a fadin Najeriya.

A wani ɓangare na shirinta na “Adopt-A-Healthcare-Facility Program” (ADHFP), Gidauniyar tana kira ga ‘yan Najeriya da su zaɓi PHCs masu buƙatar shiga cikin shirin da gaggawa. Gangamin zaɓen PHCs ɗin, wanda aka fara a ranar 4 ga watan Nuwamba kuma zai gudana har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2024, na da nufin magance babban giɓi a fannin kiwon lafiya a matakin farko na Najeriya.

Wannan shiri, wanda ƙungiyar masu zaman kansu ta Lafiya ta Najeriya (PSHAN) ta gudanar, ya biyo bayan nasarar da gidauniyar ta yi na farfaɗo da PHC guda hudu a jihar Edo, tare da ƙarin cibiyoyi 14 da ake kan aikin su. Yanzu, an mayar da hankali a gudanar da aikin a duk faɗin ƙasar, tare da ƙarfafa al’ummomin su zaɓo wuraren da ba su da wadata a cikin ƙananan hukumominsu.

Tare da akwai sama da 30,000 PHCs a duk faɗin ƙasar, an iyasta kashi 80 cikin ɗari ba su da wadata, wanda hakan yana barin miliyoyi – musamman mata da yara—masu rauni ga rashin isasshen kiwon lafiya. Adadin mace-macen mata masu juna-biyu a Najeriya ya kasance a cikin mafi girma a duniya, yayin da ɗaya daga cikin mata 22 ke fuskantar haɗarin mutuwa a sanadiyyar matsalolin da suka shafi haihuwa.

Dokta Nonye Egekwu, Daraktan Agaji na Lafiya a Gidauniyar, ya jaddada mahimmancin shirin, yana mai cewa:
“Fara farfaɗo da Cibiyoyin Kiwon Lafiyar mu na Farko yana da mahimmanci don magance ƙalubalen kiwon lafiyar Najeriya a matakin al’umma. Ta hanyar ADHFP, mun sadaukar da kai don mayar da waɗannan cibiyoyi zuwa wurare masu daraja na duniya waɗanda za su iya ba da kulawa da tallafi ga iyalai na Najeriya.”

Shirin ADHFP yana nuna yuwuwar haɗin gwiwar jama’a da masu zaman kansu don magance ƙalubalen tsarin kiwon lafiya. Yana ba wa mutane da ƙungiyoyi damar ɗaukar PHCs, haɓaka su da abubuwan more rayuwa, kayan aiki, da ma’aikata. Wannan yunƙurin ya yi daidai da manufofin kiwon lafiya na ƙasa na Najeriya, kuma yana tallafa wa ajandar gwamnati don ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na farko.

Gidauniyar tana kira ga al’umma, masu ruwa da tsaki a harkar lafiya, da sauran jama’a da su taka rawar gani ta hanyar zaɓar PHCs masu buƙatar kulawar gaggawa. Za a iya ƙaddamar da zaɓi PHCs da za a gyara ta hanyar shafin intanet na Gidauniyar kamar haka: http://aigimoukhuedefoundation.org/adhfp.

Aigboje da Ofovwe Aig-Imoukhuede ne suka kafa gidauniyar, tana mai da hankali kan sauya ayyukan hidimar jama’a da faɗaɗa damar samun ingantaccen kiwon lafiya na farko a Afirka, ta hanyar ba da kuɗi, tallafin shawarwari, da shirye-shirye na haɓaka iya aiki, yana tallafawa ayyukan sake fasalin a cikin sassan jama’a.

Don ƙarin bayani, ziyarci http://aigimoukhuedefoundation.org.

Aig-Imoukhuede Foundation Launches Campaign to Transform Nigeria’s Primary Healthcare Centres

The Aig-Imoukhuede Foundation, a leading non-profit organisation committed to improving public service delivery in Africa, has announced a nationwide campaign to revitalise Primary Healthcare Centres (PHCs) across Nigeria.

As part of its Adopt-A-Healthcare-Facility Programme (ADHFP), the Foundation is calling on Nigerians to nominate PHCs in urgent need of intervention. The nomination campaign, which began on November 4 and runs until December 31, 2024, aims to address the critical gaps in Nigeria’s primary healthcare system.

This initiative, facilitated by the Private Sector Health Alliance of Nigeria (PSHAN), follows the Foundation’s successful revitalisation of four PHCs in Edo State, with 14 more centres in the pipeline. Now, the focus has shifted nationwide, encouraging communities to spotlight under-resourced facilities in their local government areas.

With over 30,000 PHCs nationwide, an estimated 80% are under-resourced, leaving millions—especially women and children—vulnerable to inadequate healthcare. Nigeria’s maternal mortality rate remains among the highest globally, with one in 22 women facing a lifetime risk of death from pregnancy or childbirth-related complications.

Dr. Nonye Egekwu, Director of Health Philanthropy at the Foundation, emphasised the importance of the initiative, stating:
“Revitalising our Primary Healthcare Centres is essential for addressing Nigeria’s healthcare challenges at the community level. Through the ADHFP, we are dedicated to transforming these centres into world-class facilities capable of providing essential care and support to Nigerian families.”

The ADHFP showcases the potential of public-private partnerships in tackling systemic healthcare challenges. It enables individuals and organisations to adopt PHCs, driving improvements in infrastructure, equipment, and staffing. These efforts align with Nigeria’s national healthcare goals and support the government’s agenda to strengthen primary healthcare systems.

The Foundation is urging communities, health stakeholders, and the public to take an active role by nominating PHCs that require urgent attention. Nominations can be submitted via the Foundation’s website: aigimoukhuedefoundation.org/adhfp.

Founded by Aigboje and Ofovwe Aig-Imoukhuede, the Foundation focuses on transforming public service delivery and expanding access to quality primary healthcare in Africa. Through financing, consulting support, and capacity-building programmes, it supports reform initiatives across the public sector.

For more information, visit http://aigimoukhuedefoundation.org.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *