Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa takwaransa na Sakkwato

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yaba wa takwaran sa na jihar Sakkwaro, Dr Ahmed Aliyu bisa ƙara samar da guraben ayyukan yi ga al’ummar Jihar Sakkwato, musamman matasa.

A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamna Lawal ya jagoranci ƙaddamar da rabon wasu babura da A Daidai Sahu da gwamnatin Jihar Sakkwato ta samar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sayo A Daidai Sahu 500, babura 1,000, da A Daidai Sahu mai amfani da lantarki guda 150 domin raba wa matasa a faɗin jihar a matsayin wani mataki na ƙarfafa tattalin arziki.

Sanarwar ta ƙara da cewa, a jawabin da ya gabatar yayin bikin ƙaddamarwar, Gwamna Dauda Lawal ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, bisa wannan gagarumin shiri. Ya ce, “Wannan shiri ne da ya dace, musamman idan aka yi la’akari da mawuyacin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki sakamakon janye tallafin man fetur da taɓarɓarewar kasuwar canji, wanda ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan.

“Ina kira ga waɗanda suka ci gajiyar wannan shiri da su yi amfani da damar da aka ba su wajen dogaro da kai da tallafa wa iyalansu, da kuma bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin yankin.

“Adaidai sahun da za a raba, masu amfani da wutar lantarki ne. Suna da muhimmanci idan aka yi la’akari a kan yanayin da duniya ke canjawa a hankali daga amfani da motocin da suka dogara da albarkatun mai. Motocin lantarki suna da kyau ga muhalli da tattalin arziki, idan aka yi la’akari da tashin farashin man fetur.

“Amfani da su a hanyar sufuri zai yi matuƙar tasiri wajen samar da guraben ayyukan yi ga matasa, wuraren cajin su da makanikan da za su samar da kayan gwaran su”

Gwamna Lawal ya ƙara tabbatar da cewa, gayyatar da aka yi masa a matsayin babban baƙo na nuni ne ga kyakykyawan alaƙar da ke tsakanin al’ummar Sakkwato da Zamfara, wanda hakan ke ƙara zamanantar da Nijeriya.

“Tare da tarihinmu, al’adunmu, da tsarin ci gaba, dole ne mu ci gaba da bada goyon baya da ƙarfafa juna a kowane lokaci don inganta al’ummarmu. Za mu ci gaba da lalubo hanyoyin haɗin gwiwa don gina kyakkyawar makoma ga jihohinmu biyu.

“Da waɗannan kalamai, ina mai farin cikin sanar da jama’a cewa, domin ɗaukakar Allah Maɗaukakin Sarki da kuma amfanin bil’adama, na ƙaddamar da rabon da babura a matsayin ƙarfafa tattalin arziki ga matasa a faɗin Jihar Sakkwato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *