Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Sabon Tsarin Ci Gaban Zamfara Na Shekaru 10

Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da sabon Tsarin Ci Gaban Jihar Zamfara na 2025 zuwa 2034, wani tsari mai dogon zango da aka gina bisa bincike, bayanai, da tattaunawa da ƙwararru domin sake fasalin jihar a shekaru goma masu zuwa.

An gabatar da shirin ne a sakateriyar JB Yakubu da ke Gusau a ranar Juma’a, a wani taron da ya tattaro manyan jami’an gwamnati, shugabannin gargajiya da na addini, da ƙwararrun masana a fannin bunƙasar tattalin arziki.

A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, gwamnatin jihar ta ɗauki kwamitin KPMG a matsayin babban mai ba da shawara domin aikin tsare-tsaren.

A tsawon watanni takwas, kwamitin KPMG ya yi aiki tare da Majalisar Zartarwa ta Jihar Zamfara da sauran masu ruwa da tsaki wajen haɗa gagarumin shirin da ya ƙunshi muhimman fannoni na ci gaba.

Da yake jawabi yayin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana wannan tsari a matsayin shiri mafi inganci da Zamfara ta samu a tarihi, wanda ya yi daidai da manyan tsare-tsaren ci gaban ƙasa da na duniya.

Ya ambaci tsarin SDG, Babban Tsarin Ci Gaba na 2050, da Ajandar 2063 ta Tarayyar Afrika a matsayin muhimman ginshiƙai da tsarin ya jingina da su.

Gwamnan ya ce, sabon Tsarin Ci Gaban ya fayyace komai dalla-dalla, yana kuma ɗauke da ma’auni da hanyoyin sa ido domin a gano yadda ake tafiya a mataki-mataki.

“Mun gina shirin ne kan bayanai ingantattu da haɗin kan jama’a. A cikin wannan tsari, muna hango Zamfara da ta zama abin misali wajen ci gaban tattalin arziki a Nijeriya, hatta a nahiyar Afrika,” in ji shi.

Ya bayyana ginshiƙan tsari guda shida da za su zama tubalin aiwatarwa: Tattalin Arziki, Ababen More Rayuwa, Jinƙai da Walwalar Jama’a, Jarin Ɗan Adam, Gwamnati Mai Gaskiya da Nagarta, Kare Muhalli da Ɗorewar Albarkatun Ƙasa.

Gwamna Lawal ya ce, jihar za ta ci gajiyar ƙarfin ta a noman zamani da albarkatun ƙasa, ta hanyar haɗin gwiwa da cibiyoyi irin su MoFI da Bankin Vi Gaban Afrika, domin ƙara yawan amfanin gona, faɗaɗa ayyuka, da rage talauci da rashin tsaro.

“A yau ba magana kawai muke yi ba — muna kafa tubalin gobe. Muna gyara makomar Zamfara. Muna mayar da fata ga matasa, kariya ga masu rauni, da damar arziki ga al’umma,” in ji shi.

Ya ce, ƙaddamar da shirin ba wata manufa ta siyasa ba ce, illa wani sabon salo da jihar ke shiga domin ceto kanta daga koma baya.

“Lokacin da Zamfara ta haɗu da ƙalubale, ba da kuka muka tashi ba. Mun tashi da hangen nesa da jajircewa ne. Wannan tsari shi ne sabuwar hanyar da za ta zame mana haske a gaba,” in ji gwamnan.

A taron, Sakataren Gwamnati na Jihar Zamfara, Mallam Abubakar Nakwada; Shugaban Ma’aikata, Mukhtar Lugga; da Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kuɗi, Abdulmalik Abubakar Gajam, sun gabatar da jawabai masu nuni da muhimmancin sabon tsarin.

SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara
05 Disamba 2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *