Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci a ƙara ƙaimi wajen addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya a daidai lokacin da ƙasar ke bikin cika shekaru 64 da samun ’yancin kai.
Jihar Zamfara na cikin jihohi shida da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta kafa a ranar 1 ga Oktoba, 1996.
Gwamna Lawal, a cikin wani saƙon fatan alheri da Mai Magana da Yawunsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Talata, ya ce ranar 1 ga watan Oktoba rana ce ta musamman domin tunawa da irin gwagwarmaya da sadaukarwar da kakanninmu suka yi wajen fafutukar tabbatar da ’yancin Nijeriya, haɗin kai da walwalar ’yan ƙasar.
Ya ƙara da cewa, a jihar Zamfara, bikin ya rabu ne kashi biyu, “kamar yadda muke gudanar da bikin cika shekaru 28 da kafuwar jiharmu”, inji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Wannan lokaci ne na duba cikin tsanaki game da halin da jihar Zamfara da ma yankin bakiɗaya ke ciki, inda aka daɗe ana fama da ƙalubalen da ba a taba ganin irinsa ba na rashin tsaro na; tabarbarewar bangaren lafiya da ilimi da matsalar abinci, da kuma lalacewar ababen more rayuwa.
“Yau rana ce da ta ba mu damar yin tunani a kan abin da mu a matsayinmu na gwamnati ke yi don canja matsayin jihar.
“A cikin shekara guda na gwamnatinmu, jihar ta samu gagarumin sauyi kuma tana kan ci gaba da samu.
“Muna samun ci gaba sosai a fannin tsaro, noma da samar da abinci, kiwon lafiya, fannin ilimi, samar da ababen more rayuwa, da sake fasalin ayyukan gwamnati da dai sauransu.
“Duk waɗannan ana samun su ne duk da ƙarancin albarkatun da jihar ke samu. Ya zuwa yanzu, manyan nasarorin da cimma sun yi daidai da ajandarmu ta “ceto”.
“A fannin tsaro, mun kafa, horarwa, da kuma samar da kayan aiki ga Rundunar Tsaron Al’umma (CPG), waɗanda ake yi wa laƙabi da ‘Askarawan Zamfara’, mun kafa Asusun Tsaron (STF), muna ba da tallafin kuɗi na wata-wata don ci gaba da ƙoƙarin hukumomin tsaro na yau da kullum wajen samar da tsaro.
“Akan ilimi, mun kafa dokar ta-baci a fannin; an warware basukan kuɗaɗen jarrabawar WAEC da NECO, wanda ya kai adadin Naira biliyan 3.4; an sake ginawa, gyarawa, da kuma samar da kayan aiki a makarantun firamare, sakandare da manyan makarantu a faɗin ƙananan hukumomi goma sha huɗu na jihar; da kuma daidaita kuɗaɗe a sauran al’amuran ilimi.
“Har ila yau, gwamnatina ta kafa dokar ta-baci a fannin kiwon lafiya, da bullo da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kyauta tare da samar da muhimman magunguna ga marasa galihu, da gyara da samar da cibiyoyin kiwon lafiya a jihar; sake farfaɗo da samar da kiwon lafiya na zamani da kuma daidaita kuɗaɗe kiwon lafiya don taimakon masu hannu da shuni da kuma ci gaba da faɗaɗa asibitin ƙwararru na Yariman Bakura wanda muke fatan ɗaukakawa zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Zamfara.
“Don bunƙasa noma a Zamfara, gwamnatina ta samar da takin zamani da sauran kayan amfanin gona don noman damina da noman rani; mun gyara tare da inganta Kwalejin Noma da Fasaha ta Bakura.
“Mun kafa cibiyar kula da ababen more rayuwa da sabunta birane don tunkarar matsalar rugujewa da rashin wadataccen ababen more rayuwa; mun fara gine-gine da ayyukan ci gaba a filin jirgin sama na Zamfara; Ana ci gaba da faɗaɗa mahaɗar Tsohuwar Kasuwa – Tankin Ruwa; Mun ƙaddamar da mahaɗar UBA – Mahaɗar Bello Bara’u; Mashigar Bello Bara’u – Titin Nasiha Pharmacy; ƙaddamar da mahaɗar UBA – Titin Gidan Gwamnati; Mashigar Bello Bara’u – Titin Gidan Gwamnati; Mahaɗar Gidan Gwamnati – Shataletalen titin Lalan. Haka zalika, mun kammala mahaɗar Dalha Bungudu – Titin Birnin Ruwa; ana ci gaba da gina shataletalen Lalan – gina mahaɗar Gidan Zuba Jari; sake gina Gidan Zuba Jari; canja wuri da gina sabon wurin shaƙatawa na zamani a Gusau; gina hanyoyin Rawayya, Furfuri, da Kurya Madaro; gina titin Gusau – Dansadau mai kisan kilomita 86; ginawa tare da inganta Fadojin Sarakunan Gargajiya a Anka, Tsafe, Zurmi, Kaura-Namoda.
“Domin jin daɗin ma’aikata, mun daidaita albashi, fansho, da basussukan ma’aikatan gwamnati da waɗanda suka yi ritaya; mun sami nasarar daidaita ma’aikatu, cibiyoyi, da hukumomi don samar da ingantaccen ayyuka; aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira 30,000.00 ga ma’aikatan gwamnati a faɗin Jiha da ƙananan hukumomi goma sha huɗu (14); gaggauta biyan albashi da fansho ga ma’aikatan gwamnati da waɗanda suka yi ritaya a kowane wata; Ba da ihsani kamar tallafi, da kuma alawus na wata goma sha uku da kyautar Sallah, wanda ba a taba ganin irinsa ba; ana ci gaba da yi wa sakatariyar J.B. Yakubu da sauran ofisoshin gwamnati kwaskwarima da samar da nagartattun kayan aiki.”