Biyo bayan hare-haren ‘yan bindiga da aka yi fama da su baya-bayan nan, Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya jajanta wa al’ummar da ‘yan bindiga suka hana zaman lafiya a yankin Zurmi da kewaye.
Lawal ya kuma jinjina wa dakarun tsaro saboda ƙoƙarin da suke kan yi na kakkaɓe ‘yan bindiga, masu garkuwa da kuma aikata ta’addanci.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris ya fitar tare da sa mata hannu, Lawal ya bayyana tsananin damuwar sa dangane da hare-haren baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka riƙa kaiwa cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi.
Ya ce duk da wannan aika-aika da mahara ke yi, rahotanni na nuni da cewa an kakkaɓe manyan kwamandoji da gogarma-gogarman ‘yan bindiga da dama a Zamfara da sauran yankunan Arewa maso Gabas.
“Gwamnatin Zamfara ta nuna damuwa sosai dangane da hare-haren da ‘yan bindiga suka kai kwanan nan a yankunan Zurmi, Maru, Tsafe da sauran yankunan jihar.
“Muna miƙa jajentawa da ta’aziyya, alhini da damuwa ga dukkan waɗanda wannan farmaki ya shafa, musamman a Ƙaramar Hukumar Zurmi, inda aka rasa rayuka.
“Gwamnatin Jihar Zamfara za ta bayar da tallafin gaggawa da kayan agaji ga waɗanda wannan hare-hare suka shafa. Kuma mu na tabbatar da cewa gwamnati ta maida hankali sosai wajen tabbatar da tsare duniyoyi da rayukan jama’a.
“Muna kuma sane da irin sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi wajen kare rayukan jama’a. Gwamnatin Jiha za ta ƙara taimaka masu da dukkan abubuwan da suke buƙata wajen yaƙi da ‘yan bindiga.”