Gwamnan Zamfara ya koka kan yadda jami’an tsaro ke tafi da aikinsu a jihar

Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya koka kan yadda ’yan sanda da sojoji suka sanya sakaci a yaƙi da ’yan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma.

Gwamna Lawal bayyana haka ne a wani jawabi kai tsaye da ya gabatar cikin a shirin SUNRISE DAILY na gidan talabijin na CHANNELS TV a ranar Talatar nan.

Ya ce, irin salon hukumomin tsaron Gwamnatin Tarayya ya sa aka samar da Rundunar Tsaron Jihar masu suna ‘Askarawan Zamfara’.

Gwamna Dauda Lawal ya ce, “Mu a matsayin mu na gwamnoni, ba mu da iko a kan sojoji, ba mu da iko a kan ’yan sanda da jami’an tsaron farin kaya, shi ya sa galibi abin ke sa mu cikin damuwa.

“Za ka ga a lokacin da muke buƙatar waɗannan dakarun tsaro, ba za a same su ba, bisa haka ne muka ga mafita kawai mu kafa rundunar mu ta kanmu.”

Gwamnan ya bayyana cewa za a iya magance ‘yan bindiga, waɗanda suka mayar da garkuwa da mutane sana’a, cikin makonni biyu idan aka yi niyyar hakan.

“A mako biyu za su zama tarihi amma ba a shirya hakan ba a siyasance, mun san su waye ’yan bindigar nan kuma mun san wurin da suke rayuwa,” inji Dauda Lawal.

Gwamna Lawal ya yi zargin cewa wasu abokan hamayyarsa na siyasa suna tattaunawa da ’yan bindiga ba da saninsa ba.

Lokacin da aka tambaye shi ko ya san ainihin waɗanda ke tattaunawa da ‘yan bindigar, sai ya ce, “Duk abin da suke yi mun sani.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *