Gwamnati ba ta musanya sunan Titin Murtala Muhammed da na Soyinka ba, inji Minista

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa wai ta canza sunan Titin Murtala Muhammed da ke Abuja zuwa Titin Wole Soyinka.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, mataimakin sa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, ya saki a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, gwamnatin ta ce ba ta taɓa tunanin canza sunan Titin Murtala Muhammed ba.

A ranar 4 ga watan Yuni, 2024 ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da wata sabuwar hanya a Babban Birnin Tarayya, Abuja, wadda aka yi wa laƙabi da “Titin Arterial N20”, wadda ta haɗa Katampe zuwa Jahi ta kuma haɗa babbar hanyar Arewa (Murtala Muhammed Expressway) zuwa babbar hanyar Arewa (Ahmadu Bello Way).

A yayin ƙaddamarwar, Ministan Babban Birnin Tarayya, Barista Nyesom Wike, ya bayar da shawarar a raɗa wa sabon titin na ‘Arterial N20’ sunan Farfesa Wole Soyinka, shawarar da Shugaban Ƙasa ya amince da ita.

Saboda haka, sabon titin ‘Arterial N20’ ne aka sanya wa sunan Soyinka, ba Titin Murtala Muhammed ba.

Shi Titin Murtala Muhammed yana ci gaba da riƙe asalin sunan sa, wanda karramawa ce ga mai girma tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Murtala Ramat Muhammed.

Idris ya buƙaci jama’ar ƙasar nan da su yi watsi da rahotannin ƙarya da ke cewa wai an sauya sunan, tana faɗin cewa “ƙage-ƙage ne kurum marasa tushe”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *