Mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a yayinda yake ganawa da mambobin kwamitin gudanarwa kan Tsarin dabarun yaki da ƙarancin abinci wanda shugaban kasa ya kafa, a fadar shugaban kasa.
Shirin yaki da tsadar abinci da bunkasa albarkatun gona na NAPM, wani bangare ne na samar da daidaito a bangaren musayar bayanai kan harkokin noma da nufin samar da tsarin cinikayya ta bai‐ɗaya a bangaren albarkatun gona
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana shirin a matsayin wani abu da aka dauki dogon lokaci ana kokarin ķyanƙyashewa, kuma a cewarsa yanzu ne lokacin da ya kamata a ci amfaninsa.
Idan ba a manta ba, a watan Maris din Bana ne gwamnatin Najeriya da takwararta ta Brazil suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin haɗin gwiwa da ake wa lakabi da Green Imperative Project (GIP), shirin na kimanin dalar Amurka biliyan 1.1 zai farfado da matsakaitan gonakin Najeriya har 774 ta hanyar amfani fasahar noma ta ƙasar Brazil don samar da dubban aiyukan ayyukan yi da bunkasa bangaren samar da kayayyakin da aka ƙera a Najeriya
Kashim Shettima ya kara da cewa tuni Shugaba Tinubu ya bai wa Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa wato NEMA damar kashe Naira Bilyan 15 don tunkarar barazanar ambaliya a lokacin damuna wanda ka iya kawo tsaiko ga harkokin noma da zamantakewa.
A nata jawabin, mai taimaka wa Shugaban Kasa a bangaren fasahar noma, Marion Moon, ta bayyana cewa babban aikin da ke gaban NAPM Shine magance hauhawar farashin kayan masarufi da amfanin noma zuwa kasa da kashi 60 daga 100 na farashin Kasa da Kasa.
Marion ta ƙara da cewa tuni suka fara atisaye a jihohi 13, inda za a kaddamar da aikin kai tsaye a watan Yunin wannan shekarar, Kuma a bayyane yake idan aka kaddamar da wannan shiri zai samar da tsarin bai ɗaya A bangaren hada-hadar kuɗaɗen jama’a da haɓaka ci gaban ƙauyuka da birane, sakamakon inganta tsarin noma da daidaita bayanai a tsakanin gwamnati da masu zaman kansu