Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’umma da gwamnatin Jihar Borno kan mummunar ambaliyar ruwa da ta auku a Maiduguri da kewaye sakamakon fashewar da madatsar ruwa ta Alau ta yi a safiyar Talata.
Ambaliyar ta lalata kadarori, gidaje, da ababen more rayuwa, tare da raba iyalai da dama da muhallan su.
A cikin wata takarda ga manema labarai da ya sa wa hannu a ranar Talata, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa: “Muna yi wa waɗanda abin ya shafa, musamman waɗanda suka rasa sana’o’i da gidajen su, addu’a.
“Muna tare da iyalan da suka rasa muhallan su, muna kuma jajanta masu a wannan mawuyacin lokaci.”
Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta umurci ma’aikatu da hukumomin da abin ya shafa da su haɗa gwiwa da Gwamnatin Jihar Borno domin samar da agaji da dukkan taimakon da ya kamata.
A yayin da take nuna alhini kan wannan asarar da aka yi, Gwamnatin Tarayya ta bayyana gamsuwar ta da jajircewar al’ummar Jihar Borno, inda ta bayyana cewa tare da goyon bayan gwamnati da ‘yan Nijeriya, za su shawo kan wannan bala’i.