Gwamnatin Tarayya ta fara himmar ƙaddamar da shirin nan na Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa, da nufin bunƙasa ɗabi’u, ɗa’a da kuma farfaɗo da al’adu a Nijeriya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin wani taron bita wanda Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) ta aka gudanar a Abuja a ranar Laraba.
A wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, ya raba wa manema labarai, Idris ya bayyana cewa ma’aikatar sa, ta hanyar NOA, ta tsara wannan gagarumin shirin ne domin dukkan ‘yan Nijeriya su samu cikakkiyar fahimta dangane da haƙƙoƙin su a ƙarƙashin tsarin mulkin ƙasa da kuma dokokin ƙasa, sannan su ma gwamnatoci a kowane mataki su san dukkan haƙƙoƙin al’umma da suka rataya a wuyan su kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
“A ɓangare ɗaya, domin tabbatar da cewa dukkan ‘yan Nijeriya su san ‘yancin su da kariyar da suke da ita a ƙarƙashin tsarin mulki da dokokin ƙasa sannan kuma gwamnatoci a kowane mataki su san duk wani nauyi na jama’a da kundin tsarin mulki ya ɗora masu. Wannan burin na farko an rubuta shi a cikin ‘Manyan Alƙawurra ‘ bakwai na Yarjejeniyar.
“A ɗaya ɓangaren kuma, a wayar da kan dukkan ‘yan Nijeriya kan dukkan nauyin da ya rataya a wuyan mu a matsayin mu na ‘yan wannan ƙasa mai girma da kyau – wanda ke nufin nauyin da ya rataya a wuyan mu ba kawai ga junan mu ba ne, har ma ga gwamnati da ƙasa. Wannan burin na biyu an rubuta shi a cikin ‘Muhimman Alƙawurra’ bakwai na Yarjejeniyar.”
Idris ya sha alwashin ci gaba da aiki gadan-gadan babu kama hannun yaro da nufin ganin an samar da ƙasa inda ‘yan ƙasa da ‘ya’yan ta suke ƙaunar juna da girmama juna.
Ministan ya ce NOA ta zama ɗaya daga cikin hukumomi masu tasiri wajen sauya tunanin jama’ar ƙasa, kawo haɗin kai a ƙasar mai jama’a daban-daban, tare da kawo jituwa da natsuwa a kowane sashe na ƙasar.
Ya ce, “Na yi murna da ganin cewa NOA a ƙarƙashin jagorancin Mista Issa-Onilu, ta ba da muhimmanci ga fasahar zamani a aikin hukumar, tana tafiya tare da halin da ake ciki a ƙarni na 21.
“NOA ta zama ɗaya daga cikin hukumomi waɗanda suka fi yin aiki da fasahar zamani a Nijeriya a yau, suna kan gaba wajen amfani da kayan aiki na fasahar zamani kamar su manhajar The Mobiliser da kuma Fasahar Komfuta (AI) da kowa ya karɓa wajen ƙara wayar da kan jama’a.
Idris ya bayyana wannan babban taron bitar a matsayin wani muhimmin mataki da ya dace, wanda aka yi hangen nesa domin samar da wata dama wajen inganta tare da ƙara wa hukumar NOA ƙaimi da nufin tsara kyakkyawar makomar Nijeriya.