Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 9.6 don biyan ma’aikata kuɗaɗen inshorar

Shugaba Bola Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 9.6 a wannan shekara, domin sabunta biyan inshorar rayuka na ma’aikata, a ƙarƙashin Group Life Assurance.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana haka a ranar Laraba, bayan kammala Taron Majalisar.

Da ya ke magana da manema labarai bayan kammala taron a Fadar Shugaban Ƙasa, Idris ya ce an amince da kuɗaɗen ne biyo bayan wata takarda da Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan ta gabatar a wurin taron.

A taron wanda shi ne na farko cikin 2024, Minista Idris ya ce za a biya kuɗaɗen a ƙarƙashin kamfanonin inshora 12 na cikin gida, domin biyan inshorar ma’aikatan da wani Ibtila’i ka iya faɗa masu a lokacin da suke kan aikin su.

“Akwai aƙalla kamfanoni 12 da za a riƙa biyan inshorar a ƙarƙashin su. Kuɗaɗe ne da aka saba bayarwa duk shekara, waɗanda kamfanonin inshora ke bayarwa ga ma’aikata.

“Saboda haka idan mutuwa ta riski wani ma’aikaci ko ibtila’i ya same shi har ya samu rauni, to waɗannan kuɗaɗe za a biya ga iyalin sa, don kada su yi fama da jidalin zaman ƙunci,” cewar ministan.

Idris ya ce Shugaba Tinubu ya amince da biyan kuɗaɗen saboda kyakkyawan muradin wannan gwamnati na inganta jin daɗin ma’aikata, domin su ƙara ƙwazo wajen yi wa ƙasar su aiki ga gaskiya kuma tuƙuru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *