Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce duk da yake tattalin arzikin Nijeriya na fuskantar ƙalubale, kwatanta shi kafaɗa-da-kafaɗa da na Venezuela da gwamnonin jam’iyyar PDP su ka yi rashin adalci ne ainun.
Ya ce: “Mu na bayyana cewa duk da yake ƙasar mu na fuskantar wasu matsaloli, waɗanda kuma wannan gwamnati ta Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin magance su, to kuma matsalolin mu ko kusa ba su kai na Venezuela ba, kamar yadda gwamnonin PDP su ka rufe ido su ka faɗa.”
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ministan ya ce: “Tattalin arzikin Nijeriya har yanzu ya na da ƙarfi sosai, kuma ana sa rai da kyakkyawan hasashen cewa zai bunƙasa da ƙarin kashi 3 cikin 100 cikin wannan shekarar.
“Tattalin arzikin mu na bayar da gudunmawar lamuni ga masu rance a cikin gida da waje.”
A ranar Litinin ce dai gwamnonin PDP su ka gudanar da taro a Abuja, inda su ka tattauna batutuwa, musamman waɗanda su ka shafi matsalar tsaro da matsalar tattalin arziki, wadda ta haifar da matsalar tsada da raɗaɗin tsadar rayuwa.
Bayan kammala taron, sun bada sanarwar cewa sun amince kowace jiha a ba ta damar kafa ‘yan sandan jiha, domin a samu a shawo kan ƙalubalen matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.
Amma a raddin da ya yi masu, sai Idris ya ce, “Mu na maraba da shawarwarin da su ka bayar waɗanda ba na son rai ba, domin ganin an magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki.”
Ya ragargaji gwamnonin da cewa sun taimaka wajen haifar da matsalar tattalin arziki.
Ya ce, “A matsayin su na shugabanni a gwamnatocin jihohi, gwammonin PDP su na da ‘yancin bayyana matsayar su kan duk wani abu da ya shafi ƙasar nan.
“To sai dai membobin Majalisar Tattalin Arziki da kuma Majalisar Zartaswa ta Ƙasa, mun yi amanna da cewa gwamnonin ba su nuna dattakon da ya kamata su nuna ba, a matsayin mu na shugabannin jama’a.
“A matsayin gwamnonin PDP, waɗanda ya kamata a ce masu shiga sahun gaban inganta tattalin arziki ne, samar da yalwa a ƙasa ga ‘yan ƙasar a jihohin su, a ce kuma sun koma su na furta kalaman ƙage da shaci-faɗi kan Nijeriya, har su na kwatanta matsalar tattalin arzikin Nijeriya da irin matsalolin da su ka dabaibaye tattalin arzikin Venezuela.
“Mu na son mu bayyana cewa duk da yake dai tattalin arzikin mu na fuskantar ƙalubale, amma ko kusa ba daidai ba ne a kwatanta matsalar Venezuela da ta Nijeriya.
“Yayin da Gwamnatin tarayya ke biyan albashi da sauran haƙƙoƙin ma’aikata kan kari, kuma harkokin gwamnati na tafiya daidai-wa-daida, ya kamata ‘yan Najeriya su tambayi gwamnonin PDP abin da su ka yi da kuɗaɗen da ake ba su.
“Saboda akwai rahoton bincike mai nuna cewa yawancin jihohin PDP sun kasa biyan ‘yan fansho kuɗaɗen su na tsawon watanni da dama, haka albashin ma’aikata ma wasu ba su biya yadda ya kamata.
“Gwamnonin PDP na ƙin biyan garatutin ma’aikatan da su ka yi ritaya.
“Haka kuma wasu gwamnonin PDP ɗin har yau sun kasa ma biyan naira 30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi, shekaru huɗu da Gwamnatin Tarayya ta fara amfani da tsarin.”