Gwamnatin Tinubu za ta dawo wa NTA da FRCN da martabar su – Minista

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da Darakta-Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama, da Darakta-Janar  na NTA, Malam Salihu Abdulhamid Dembos, da sauran jami’ai a lokacin da ministan ya kai ziyarar aiki a NTA da FRCN Kaduna a ranar Juma’a

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce gwamnati mai ci yanzu a ƙarƙashin Bola Ahmed Tinubu ta ƙudiri aniyar aiwatar da wasu tsare-tsaren gyara da za su dawo da martabar da aka san mashahuran kafafen watsa labarai biyu ɗin nan biyu da su, wato Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA) da Hukumar Gidajen Rediyon Tarayya (FRCN).
Hadimin musamman na ministan kan harkokin yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya faɗa a cikin takardar sanarwa ga manema labarai cewa Ministan ya sha wannan alwashin ne a Kaduna a ranar Juma’a lokacin da ya kai ziyarar aiki a ofishin hukumomin biyu.
A yayin da ya ke magana kan babbar rawar da gidan Rediyon Tarayya na Kaduna da gidan talbijin na NTA Kaduna su ke takawa wajen jan akalar ra’ayin jama’a da watsa labarai da ɗabbaka musayar al’adu, Ministan ya ce kafafen biyu sun samu koma-baya a ‘yan shekarun nan da su ka gabata saboda watsi da su da aka yi, da rashin tarbiyyar aiki, da tsofaffin wuraren aiki da kayan aiki, wanda hakan ya karya alkadarin su wajen yin shirye-shirye da taka muhimmiyar rawa. 
Sai dai kuma Idris ya bada tabbacin cewa gwamnatin Tinubu za ta farfaɗo da kafafen kuma ta mayar da su kan gaba a aikin rediyo da na talbijin a Nijeriya.
Ya ce: “Yadda za a iya mayar da NTA da FRCN matsayin wakilan ƙwarai a tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya sosai, tilas sai mun yi la’akari da babbar gazawar su a yanzu a fagen da ke cike da gasa, da amfani da basira, da amfani da fasahohin zamani.
“Dalilin zuwa na nan tare da Darakta-Janar na NTA da na FRCN shi ne domin mu nemo cikakkiyar hanyar da za mu bi don magance waɗannan matsalolin, wanda ya na kan gaba cikin abubuwan da mu ka ba muhimmanci. 
“Za mu duba dukkan zaɓi da ke gaban mu domin tabbatar da cewa mun dawo da martabar da NTA da FRCN su ka rasa.” 
Ministan ya ce matsalar FRCN a matakin ƙasa da na jihohi ya ma fi ta’azzara, musamman ma a Rediyon Nijeriya, Kaduna, wanda ya bayyana da cewa “a da wuri ne mai daraja na yaɗa labarai wanda ya samar da zaƙaƙuran ma’aikatan rediyo.”
“Hakika, Rediyo Nijeriya Kaduna na buƙatar a farfaɗo da shi da gaggawa. Babu shakka za mu ɗauki mataki da sauri a wannan aiki na ceto,” inji shi.
Idris ya ce a lokacin da ya kama aiki, ya samu kiraye-kiraye masu yawa daga sassa da dama masu ruwa da tsaki a kan lalacewar kafafen biyu, ya na mai nanata cewa lallai aikin da ke gaban sa shi ne tabbatar da cewa an yi wa NTA da FRCN garambawul domin su cimma manufofin kafa su. 
Ya ce: “Ina tabbatar wa da shugabanni da ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki a NTA da FRCN cewa Shugaba Tinubu ya naɗa Malam Salihu Abdulhamid Dembos da Dakta Mohammed Bulama a matsayin Darakta-Janar na NTA da FRCN ne bayan cikakken nazari kan ƙwarewar su wajen iya kawo kyakkyawan sauyi a hukumomin biyu waɗanda babu hukumomin aikin talbijin da rediyo kamar su wajen girma a Nijeriya da ma Afrika baki ɗaya.
“A shirye na ke in duba kowace dama da ke akwai wadda za ta bayar da duk abin da ake buƙata don tabbatar da cewa sama wa NTA da FRCN kayan aiki na zamani, bai wa ma’aikatan su cikakkiyar horaswa da kuma biya masu haƙƙoƙin aiki an yi su da gasken gaske.”
Ministan ya ce ya kamata hukumomin yaɗa labaran biyu su tashi tsaye su rungumi yanayin aikin jarida wanda zamani ya kawo wajen aiki da kayan fasaha na zamani idan har su na so a yi gogayya da su, su inganta kyawun aiki, kuma saƙwannin su su kai ga ɗimbin masu kallo da masu saurare.
Waɗanda su ka take wa Ministan sawu a lokacin wannan ziyara dai su ne Darakta-Janar na NTA, Salihu Abdulhamid Dembos, da takwaran sa na FRCN, Dakta Mohammed Bulama. 
Ban da hedikwatar tashoshin biyu, sun duba muhimman kayan aikin tashoshin biyu da ke cikin garin Kaduna da kuma garin Jaji a babban titin Kaduna zuwa Zariya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *