Gwamnatin Zamfara ta musanta hana gasa burodi

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewa babu inda gwamnatin sa ta hana yi ko sayar da biredi a duk faɗin jihar.

Wannan ya biyo bayan wata sanarwa ce da ƙungiyar masu gidajen biredi ta jihar Zamfara ta fitar, inda suka shelanta dakatar da gasa biredin sakamakon haramta tallar sa da gwamnatin ta yi a bisa babura, wanda kuma gwamnatin ta ce ta yi haka ne don ta katse hanyoyin da ake kai wa ‘yan ta’adda biredin.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnatin ba ta ɗauki wannan matakin da wata mummunar manufa b ne, illa don ta toshe hanyoyin da ake kai wa ‘yan ta’adda kayan masarufi a duk faɗin jihar.

Sanarwar ta Idris ta ƙara da cewa gwamnatin ta haramta sayar da biredi da man fetur a wuraren da ta’addancin ya yi ƙamari ne don a toshe hanyoyin da ‘yan ta’addan ke samun kayan masarufi.

Sanarwar ta ƙara sa cewa, “Gwamnatin jijar Zamfara na so ta yi ƙarin haske game da surutan sa ke yawo, inda ake zargin cewa gwamnatin ta hana masu gidaje biredi yi a jihar.

“Gwamnatin na ƙalubalantar waɗannan labarai da cewa ba gaskiya ba ne, wanda ke kuma jawo ruɗani a tsakanin jama’a da su kan su masu gidajen biredin.

“Gwamnatin jihar Zamfara ba ta da wata niyya ta tsoma baki a harkar gasawa ko sayar da biredi, wanda biredi a yanzu ya zama shi ne kusan abincin kowane gida.

“Bugu da ƙari, mu na so mu tabbatar wa al’umma cewa kullum ƙoƙarin gwamnati, shi ne fito da hanyoyin da za ta inganta harkokin kasuwanci da hanyoyin cin abinci ga al’ummar ta. Mu na sane da irin gudumawar da ƙananan masana’antu ke bayarwa ga ci gaban tattalin arziki, kuma mun jajirce wajen ganin mun ƙarfafa masu gwiwa don cimma nasarar su.

“Kuma duk da haka, mun fito da wasu hanyoyi da dama na yaƙar ‘yan ta’adda masu kawo mana ruɗani a wasu sassan jihar nan.

“Waɗannan hanyoyi kuwa, sun haɗa da haramta sayar da biredi da man fetur a wasu wurare da ba a natsu da su ba, ba domin komai ba, sai don a takura wa waɗannan shaiɗanu, domin sun dogara ne da waɗannan muhimman abubuwa wajen aiwatar da Ta’addancin su.

“Gwamnatin jihar Zamfara na da fatan cewa sakamakon aiwatar da wannan haramci, za ta iya dawo da zaman lafiya a waɗannan wurare, don kare rayuka da dukiyar jama’a. Wannan haramci da aka ambata, yana daga dabarun da ake sa ran cimma nasarar wannan yaƙi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *