Daga Abubakar Musa
Ministan tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila, Israel Katz, ya bayar da umarni ga sojojin na HKI da su fara shirin fitar da Falasdinawa daga Gaza “ba tare da tursasawa ba,” inda hakan ke nuni da amfani da kalaman Trump na cewa yana da niyyar kasancewa “mai iko” da yankin.
“Na bayar da umarni ga IDF (rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila) da ta tsara shirin yadda duk wani wanda ya ke a Gaza da ke so ya bar ta zai bari, zuwa duk wata kasar da ke so ta karbe su.” Kamar yadda The New Arab ta ruwaito cewa Israel Katz ya rubuta a shafin X.
“Shirin zai hada da zabin ficewa ta kasa, da kuma tsari na musamman domin ficewa ta ruwa da ta sama.”
Wannan na zuwa ne a yayin da manyan jami’an gwamnatin Trump suka janye daga ra’ayin shugaban kasar biyo bayan fusata da kasashen duniya suka yi.
Kalamansa, wadanda ya yi biyo bayan ganawarsa da Firaministan HKI Benjamin Netanyahu a Washington, Falasdinawa da kasashen duniya sun yi Allah wadai da su amma masu tsatstsauran ra’ayi a HKI suke amfani da su, wanda hakan ke barazana ga yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas.
Kuma a yanzu haka, ‘yan HKI din na cigaba da hare-harensu a fadin Yamma da gabar kogin Jordan da aka mamaye a yayin da Falasdinawa ke cigaba da tantance asarorin da yaki na sama da watanni 15 ya haifar a Gaza.