Hukumar yaki da safarar mutane a Nijeriya ta ceto mutane sama da 20,000 a shekaru 22

Hukumar yaki da safarar mutane a Nijeriya (NAPTIP) ta bayyana cewa ta kama masu laifi sama da 600 tare da ceto mutane sama da 20,000 wadanda safarar mutane ya shafa tun shekarar 2003.

Kamar yadda PM News ta ruwaito, kwamandan hukumar ta NAPTIP yankin Benin, Ganiu Aganran, ne ya bayyana haka a ranar Litinin a Benin yayin da ake bude taron wayar da kai na kwanaki biyu ga hukumomin tsaro a jihar Edo.

Kwamitin taimako ga mutunta mata (COSUDOW) ne ya shirya taron tare da hadin gwiwar hukumar ta NAPTIP domin karfafa gwiwar jami’an tsaro wajen yaki da safarar mutane (TIP).

“NAPTIP na aiki ba tare da gajiyawa ba wajen ganin masu safarar mutane sun fuskanci hukunci kuma an taimaki wadanda aka ceto.” Kamar yadda ya bayyana.

Kwamandan yankin ya bayyana rigakafi, hukunci, kariya, hadin gwiwa da tsare-tsare a matsayin matakai biyar da hukumar ke amfani da su domin magance mummunan al’amarin.

“Matakan NAPTIP sun hada da bincike da ya shafi leken asiri, hadin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma aikin taimako ga mutanen da aka ceto domin tabbatar da an yaki safarar mutane da kyau.” Kamar yadda ya kara da cewa, inda ya nuna damuwar kasancewar Edo daya daga cikin yankunan Nijeriya da al’amarin ya shafa sakamakon talauci, rashin aikin yi, rashin ilimi da kuma rashin karfin tabbatar da doka da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *