Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta sanar a ranar Alhamis cewa ta bayar da sammacin kame Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaro Yoav Gallant.
A cikin sanarwar da ta bayar, kotun ta ICC ta jaddada cewa, ba sai an sami amincewar Isra’ila da hurumin kotun kafin sammacin ya kasance mai inganci ba.
Kotun ta zargi Netanyahu da Gallant da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama, ciki har da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.
Zargin dai ya samo asali ne daga matakan da suka dauka a lokacin kisan kiyashin da sojin Isra’ila ke yi wa a Gaza, wanda ya janyo cece-kuce da kuma tofin Allah tsine a duniya.
Kotun ta ICC, wacce aka kafa domin gurfanar da mafi munin keta dokokin kasa da kasa, ta lura cewa ta yanke hukuncin ne bisa bincike na farko da shaidu.
Yarjejeniyar kafa kotun ta ICC da aka kafa a birnin Rome hade da hukunce-hukuncen shari’o’i na baya da suka hada da sammacin kama shugabannin kasashe da ke kan madafun iko ya tilasta wa dukkanin kasashe 124 da suka rattaba hannu a kan kotun ICC da su kama tare da mika duk wani mutum da ke cikin sammacin kama shi idan ya taka kafarsa a yankinsu.