Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da Ƙungiyar Kakakin Labarai (spokesmen), inda ya buƙace su da su yi amfani da ilimi, gogewa, da guraben da ake da su a ƙungiyar.
Ministan ya yi magana ne a ranar Alhamis a gaban tawaga daga Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ƙarƙashin jagorancin Farfesa Emmanuel Dandaura, muƙaddashin shugaban cibiyar.
Ministan ya bayyana rawar da Kakakin Labarai su ke takawa a matsayin masu tace labarai a kafofin su daban-daban, “ko a cikin gwamnati, sashi masu zaman kan su, sashen ci gaba, ko kuma sashen sa kai, masu magana da yawun su na da muhimmiyar rawa wajen ƙwato martabar ƙungiyoyin su da al’umma a cikin dogon lokaci.”
Ya ce hakan ne ya sa ma’aikatar sa ta haɗa kai da cibiyar wajen shirya wannan taro.
Idris ya kuma buƙaci Kakakin Labaran da su tuna cewa domin samun nasara a muhimman ayyukan da aka ba su, dole ne su kasance su na da cikakkun kayan aiki da horaswa da kyawawan ɗabi’u da za su riƙa nuna ƙungiyoyin su da ƙasar su da kyau.
Ya buƙace su da su ware ranakun 25 – 28 ga Maris, 2024, a kalandar su domin halartar taron.
Bugu da ƙari, ya yaba wa wannan shiri kuma ya ce ya zo a daidai lokacin da ya dace da gwamnati za ta inganta Yarjejeniyar Ƙimar Ƙasa.
Ministan ya ba da tabbacin cewa masu magana da yawun za su ɗauki saƙon, su yi amfani da shi, sannan su yaɗa shi ta hanyar ƙungiyar su.
Hoto: Idris tare da muƙaddashin shugaban NIPR, Farfesa Emmanuel Dandaura