Idris ya jajanta wa al’ummar Neja da iyalan mutum 59 da suka mutu sakamakon fashewar tankar mai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a ranar Litinin ya jajanta wa al’ummar Jihar Neja bisa rasuwar mutane 59 a wani haɗarin mota da ya ritsa da su a hanyar Bida-Agaie-Lapai ranar Lahadi.

A cikin saƙon ta’aziyya da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya sanya wa hannu, ministan ya ce lamarin ya girgiza Jihar Neja da ƙasa baki ɗaya.

Ya yi addu’ar Allah ya ba iyalan mamatan ikon jure wannan babban rashin.

Idris ya ce: “Ina miƙa ta’aziyya ta ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja da iyalai, abokai da ‘yan’uwan mutane 48 da suka rasa rayukan su a wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Bida-Agaie-Lapai a Jihar Neja da sanyin safiyar Lahadi, 8 ga Satumba, 2024.

“Wannan mummunan lamari ya girgiza ɗaukacin Jihar Neja da ma ƙasa baki ɗaya kuma ina yi wa duk waɗanda abin ya shafa a wannan lokaci mai zafi addu’a. Don haka ina taya al’ummar Jihar Neja da ma Nijeriya baki ɗaya alhinin wannan babban rashi.

“Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu kuma Allah ya bai wa iyalan su juriyar wannan rashi mara misaltuwa.”

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), reshen Jihar Neja, Mista Kumar Tsukwan, ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa dukkan waɗanda abin ya shafa maza ne, kuma da ba a iya tantance motocin da abin ya shafa ba saboda tsananin ƙonewar su.

Tsukwan ya bayyana cewa lambar mota ɗaya kacal ce aka iya tantancewa, yayin da ba a gane lambobin sauran ba.

Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 4:30 na safe kuma an kai rahoton lamarin ga sashin Lapai na FRSC da ƙarfe 4:40 na safe.

Ya ce: “Motar tankar man da ke ɗauke da mai daga Legas zuwa Kano tana gudu sosai, inda ta ƙwace ta faɗi ta kama da wuta yayin da wutar ta shafi wata tirela da ke ɗauke da shanu da mutane tare da wasu motoci biyu a baya. Dukkan motocin guda huɗu sun ƙone ƙurmus.”

“An ruwaito cewa sai da ɗaya daga cikin fasinjojin tirelar da ke ɗauke da mutane da shanun ya ankarar da direban cewa akwai wuta fa a gaban su amma sai direban ya amsa da cewa taya ce kawai ke ƙonewa, kuma da isa wurin tankar da ke ci da wuta, wutar ta kama tirelar da kuma wasu motoci biyu.”

A cikin wani ƙarin bayani, Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta ce adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru daga 48 da aka bayyana da farko zuwa 59 saboda an gano wasu gawarwaki wajen ci gaba da ceto yayin da ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa da ya ƙone sosai ya mutu a Cibiyar Kula da Lafiya ta Tarayya da ke Bida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *