A daren jiya, sojojin Isra’ila sun kai hare-hare mafi muni a tarihin rundunar saman Isra’ila cikin Siriya, bayan faduwar gwamnatin Bashir Al-Asad a makon jiya.
Abin da kafafen watsa labarun Isra’ila suka fada ke nan.
-Sun Rusa da kona dukkanin jiragen sama na yaki da Siriya take da su.
Sun Rusa da kone kusan mafi yawancin tankokin yakin Siriya.
Sun rusa mafi yawancin jirage masu saukar Angulu na yaki da Siriya take da su.
Sun lalata cibiyar bincike da nazari ta soja da ke kusa da Damascus, babban birnin ƙasar.
Sun kutsa da tankokinsu na yaki da sojoji zuwa kilomita 25 cikin Siriya.
Sun kone dukkanin makaman kakkabo jiragen sama mallakin Siriya.
Wata muhimmiyar tambaya a nan ita ce, waye kawar da Bashir Asad daga mulki ya amfana?
Mai karatu mu hadu a sashen kwament.