Jihar Kebbi za ta dauki nauyin aurar da mutane 300

Gwamnatin jihar Kebbi ta bayyana shirinta na daukar nauyin aurar da mutane 300 a jihar.

Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoton Sahara Reporters, bukin auren an shirya za a yi shine a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Shirin, wanda ke da niyyar taimakon marasa karfi a jihar, an yi shine da taimakon gidauniyar “Nafisa Nasir Charity Development Foundation” (NANAS) wadda gidauniya ce wadda ba ta gwamnati ba.

Alhaji Suleiman Argungu, wanda shine shugaban kwamitin tsarawa, ne ya bayyana haka ga ‘yan jaridu a Birnin Kebbi, kamar yadda NAN ta ruwaito.

Alhaji Suleiman ya bayyana cewa aurar da mutane masu yawan yana daga cikin abubuwan da gwamna Nasir Idris ya mayar da hankali a kai wajen ganin duk shekara an shirya irin wadannan bukukuwa domin ganin an taimaki wadanda ba su da halin yin aure.

Alhaji Suleiman ya bayyana cewa gwamnatin za ta bayar da N180,000 a matsayin sadaki ga kowacce amarya, inda kudin suka kama naira miliyan 54 ga mutane 300. Bayan sadaki, gwamnatin za ta samar da abubuwa masu muhimmanci ga wadanda aka aurar din kamar kayan daki da kayan abinci domin taimakon rayuwar aurensu.

Domin tabbatar da lafiya da kuma bin ka’ida dangane da wadanda aka aurar din, an kafa kwamitoci daban-daban domin kula da abubuwa kamar gwajin juna biyu, gwajin kwayar halitta (Genotype), gwajin HIV/AIDS da sauran abubuwa da suke muhimmai kafin aure.

“Gwamnatin gwamna Idris za ta bayar da sadakin N180,000 ga kowacce amarya da ta fito daga kowacce karamar hukuma 21 a jihar.

“Za a samar da karin wasu abubuwan kamar kayan daki da abinci ga wadanda aka aurar din domin taimakon aurensu.

“Za a gudanar da daurin auren bayan tattaunawa mai fadi da malaman addinin Musulunci domin dacewa da koyarwar Annabi Muhammad (S).” Kamar yadda Alhaji Suleiman Argungu ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *