Jihar Taraba ta mayar da shanu 198 da aka sace ga masu su

Jihar Taraba ta mayar da shanu 198 wadanda rundunar 6 Birget na sojin Nijeriya da kuma mafarautan kauye suka kama a jihar da aka sato ga masu su.

Sojojin na rundunar 6 Birget a ranar 27 ga watan Janairun 2025 ne suka kama shanu 222 da kuma raguna 58 a kauyen Namnai da ke karamar hukumar Gassol a jihar ta Taraba da aka yi imanin cewa an sato su ne daga Kamfanin Zurak da ke jihar Filato, kamar yadda kafar watsa labaru ta Thisday ta ruwaito.

Mutum uku da ake zargi, Sabiu Lawal, Haruna Ayuba da Yusuf Mukawo, wadanda duka sun fito ne daga Kamfanin Zurak rundunar ta kama su dangane da sace shanun.

Yayin da ya ke mika shanun ga masu su a ranar Alhamis a Jalingo, shugaban kwamitin mika shanun da aka sato ga masu su, Dakta Aminu Jauro Hassan, ya bayyana cewa kwamitin ya iya tabbatar da masu shanu 198 a cikin shanu 222.

Dakta Hassan ya bayyana cewa kwamitin ya tantance kungiyoyin masu shanu 52 ta amfani da hanyar gargajiya domin tabbatar da ikirarin su na mallakar shanun inda a yanzu ake da sauran shanu 24.

Shugaban kwamitin ya kara da cewa masu shanun sun fito ne daga karamar hukumar Ardo Kola da ke jihar Taraba inda ya tabbatarwa jama’a cewa kwamitin zai cigaba da sanarwa ga jama’ar kasa domin masu shanun da suka rage su zo garesu.

Hassan ya lissafo wasu mambobin kwamitin wadanda suka hada da shugaban karamar hukumar Ardo Kola, Gassol, Lau da Karim Lamido da kuma wakilan kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da kuma hukumomin tsaro.

Sai kuma ya yi yabo ga gwamnan jihar, Dakta Agbu Kefas, domin kokarinsa wajen ganin an mayar da shanun ga masu su na hakika.

A yayin da ya ke na shi jawabin, shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a jihar Taraba, Alhaji Yau Ibrahim, shi ma ya yi yabo ga gwamnan jihar Kefas domin dawo da shanun ga masu su na hakika, inda ya ce hakan zai kara zaman lafiya a tsakanin mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *