Kasar Sin za ta bayar da taimakon jin kai ga iyalai 60,000 da ke Gaza

Hukumar cigaban kasa-da-kasa ta kasar Sin ta bayyana cewa za ta bayar da taimakon jin kai ga iyalai 60,000 da ke Gaza, kamar yadda wani rahoto na The New Arab ya nuna.

“A duk yadda al’amari ya juya, Sin za ta cigaba da goyon bayan mutanen Falasdinu a kokarinsu a yunkurinsu da ke kan ka’ida na dawo da hakkokinsu na kasarsu na doka da kuma warware al’amarin da ya shafi Falasdinawa ta hanyar samar da kasashe guda biyu.” Kamar yadda hukumar ta shaida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *