Daga Abubakar Musa
Kasashe kawayen kasar Amurka da wadanda ba kawayenta ba take sun yi watsi da shawarar shugaban kasar Amurka Donald Trump wadda ke cike da takaddama na mallakar Gaza bayan tayar da bakidaya al’ummar yankin; tare kuma da haifar da Allah wadai daga fadin duniya.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Press TV ta ruwaito, yayin wani taron hadin gwiwa da Firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Talata, Trump ya ce Amurka za ta karbi iko da zirin Gaza – mai yiwuwa da karfin soji – domin Kirkirar “Yankin bakin teku a Gabas ta tsakiya.” Tun da farko ya yi shawarar Falasdinawa za a iya zaunar da su a wani wurin.
Wadannan kalamai na shi take suka haifar da Allah wadai daga kasashen duniya, inda kasashen turai da suke kawayen Amurka, Saudi Arabiya, Jordan da Misra suka sake nanata kiransu na samar da mafita ta hanyar samar da kasashe biyu.
Ma’aikatar harkokin kasashen wajen Saudi Arabiya ta bayyana a cikin wani jawabi cewa yarima Mohammed bin Salman ya bayyana matsayar masarautar “a bayyane kuma a fili” ta yadda ba a bukatar wata fassara ko da kadan ce.”
Ministan harkokin kasashen wajen Misra Bader Abdelatty ya yi kira da a sake gina yankin ba tare da bata lokaci ba “ba tare da Falasdinawa sun tashi ba.”
Ministan harkokin kasashen wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana abinda Trump ke yunkurin ganin an aiwatar da “abinda ba za a amince da shi ba.”
“Bai dace ba ko tattaunawa a kan shi a yi.”
Ministocin kasashen waje da dama na kasashen turai su ma sun nuna kin amincewarsu da Trump, inda suka nuna cewa tayar da Falasdinawa ya keta dokar kasa-da-kasa.
Ministocin harkokin kasashen wajen Spain, Jamus, Faransa da Birtaniya duk sun nuna rashin amincewarsu da tayar da Falasdinawa daga yankin Gaza, Rasha da kasar Sin suma sun yi watsi da tayar da Falasdinawa zuwa wani wuri domin Moscow da Beijing sun yi imanin cewa samun mafita a Yammacin Asiya zai faru ne kawai idan an samar da kasashe biyu.