Kasashen Faransa, Ingila da Jamus sun yi kira ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Kasashen Faransa, Ingila da Jamus a ranar Laraba sun nemi Haramtacciyar Kasar Isra’ila (HKI) da ta tabbatar da “rashin tsaiko” ga shigar da kayayyakin taimakon jin kai zuwa yankin Falasdinawa na Gaza da yaki ya yiwa illa, inda suka yi gargadin yin amfani da taimakon jin kan a matsayin “makamin siyasa.” Kamar yadda The New Arab ta ruwaito.

Bayan tsagaita wutar da aka samu a ranar 19 ga watan Janairu wadda ke fuskantar matsaloli an ga tururuwar shigowar kayayyakin taimakon jin kai zuwa cikin Gaza, kafin ranar Lahadi inda HKI din ta sanar da cewa za ta dakatar da shigowar kayayyakin har sai kungiyar fafutika ta Falasdinawah ta Hamas ta amince da bukatun ta na tsawaita tsagaita wutar.

Dakatarwar wadda HKI ta yi a karshen mako, kamar yadda kafar ta ruwaito, na da niyyar tursasawa ne ga Hamas da ta amince da wani tsari na daban na tsagaita wutar makonni shida bayan tsagaita wutar wadda ke fuskantar matsaloli, inda ita kuma Hamas ta yi watsi da hakan.

“Muna kira ga gwamnatin Isra’ila da ta yi abinda ya dace kamar yadda ya ke a kasa-da-kasa wajen ganin kayayyakin taimakon agaji na shiga da sauri, ba tare da ragewa, ba tare da matsala ba kuma tare da hanawa ba ga al’ummar Gaza.” Kamar yadda kasashen suka bayyana a cikin jawabin su na hadin gwiwa.

“Dakatar da kayayyakin taimakon agaji da ke shiga Gaza kamar irin wannan da gwamnatin Isra’ila ta bayyana na iya barazana ga dokokin taimakon jin kai na kasa-da-kasa.” Kamar yadda suka bayyana.

“Taimakon jin kai bai kamata ya dogara a kan tsagaita wuta ba ko kuma a yi amfani da shi a matsayin makamin siyasa ba.”

Kasashen turai din uku sun bayyana yanayin da ake ciki a Gaza da wanda ya “ta’azzara.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *