Kotun Ƙoli za ta saurari ƙarar zaɓen gwamnan Kano ranar Alhamis

Kotun Ƙolin Najeriya ta sanya ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba domin sauraron ƙarar da aka shigar kan zaɓen gwamnan jihar Kano.

Gwamna Kabir Abba Yusuf na jam’iyyar NNPP na kalubalantar hukuncin kotun daukaka ƙara da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 11 ga Maris.

Lauyan Gwamna Yusuf, Barista Bashir Tudun Wazirci, ya tabbatar wa BBC cewa an ba su sanarwar fara sauraron ƙarar a matsayinsu na tawagar lauyoyin da ke wakiltar gwamnan da jam’iyyarsa.

Wannan ne karon farko da kotun za ta fara zama, inda za ta fara jin bahasi, yayin da har yanzu akwai muhimman takardun da ba a kai wa kotun ba.

“Har yanzu akwai takardun da muka [NNPP] ba su [APC] da ba su dawo mana da martani ba tukunna, kuma mu ma muna da damar sake yin martani idan suka dawo da su,” in ji Bashir Tudun Wazirci.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa Gwamna Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya tsaya takarar gwamna.

Amma tabbataccen kwafin hukuncin, wanda ya bayyana kwanaki kaɗan bayan zaman kotun, ya kunshi bayanai masu karo da juna game da hukuncin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Duka ɓangarorin biyu dai sun yi iƙirarin cewa hukuncin ya tabbatar da nasarar da suka samu a zaben.

Sai dai jam’iyyar NNPP ta shigar da ƙara a gaban kotun ƙoli, inda take ƙalubalantar hukuncin kotun daukaka ƙara da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *