Hoto: Wani yanki na zirin Gaza
Tsaunin abubuwan da suka rushe mai yawan gaske ciki harda makaman yaki wadanda ba su tarwatse ba da Isra’ila ta bari a mummunan yakin ta a zirin Gaza zai iya daukar kimanin shekaru 14 kafin a kwashe su, kamar yadda wani jami’in majalisar dinkin duniya ya bayyana a ranar Juma’a.
Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, Pehr Lodhammar, babban jami’i a hukumar majalisar dinkin duniya da ke kula da harkokin da suka shafi bam (UNMAS), ne ya shaida a wani taro a Geneva cewa yakin ya bar tarin rusassun abubuwa kimanin tan miliyan 37 a wajen wanda ya ke birni ne, kuma yanki mai cinkoson jama’a.
Ya ce duk da ya ke abu ne mai wuya a iya gane yawan kayan yakin da ba su fashe ba a Gaza, an yi kiyashin cewa zai iya daukar shekaru 14 a karkashin wasu sharudda kafin a iya kwashe rusassun abubuwan, ciki har da bungaru daga gine-ginen da aka lalata.
“Mun san cewa akwai abubuwan fashewa da aka harba akalla kashi 10 cikin 100 da ba za su yi nasarar fashewa ba su kuma kasa yin aiki.” A cewar sa, “Muna maganar shekaru 14 ne na aiki da manyan motoci 100.”