Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Lura da Harkokin Yaɗa Labarai, ya nuna rashin amincewa dangane da ƙarancin kuɗaɗen da kwamitin ya ce Gwamnatin Tarayya ta ware wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da kai, a Kasafin 2024.
Shugaban kwamitin, Sanata Kenneth Eze ne ya nuna damuwa da rashin amincewa dangane da ƙarancin kuɗaɗen, a lokacin da Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris ya bayyana a gaban kwamitin, domin ya kare kasafin ma’aikatar sa, a ranar Talata, a Abuja.
“Haba jama’a, ai waɗannan kuɗaɗe cikin cokali bai yiwuwa a ce da su kaɗai za a yi amfani har a samu biyan buƙatar yada manufofin ƙasar mu. Muddin waɗannan kuɗaɗen ne aka ware wa wannan ma’aikatar, to ba inda za mu iya cimma gaci. Ta yaya za a iya wayar da kan jama’a ta hanyar yaɗa labarai da kyawawan manufofi da waɗannan kuɗaɗe ƙalilan?
“Ma’aikatar Yaɗa Labarai fa wuri ne mai muhimmancin da wajibi ne a yi wa wurin riƙon kazar kuku, ba riƙon sakainar kashi ba. Ina magana idan har fa ana so a samu biyan buƙatar samun nasarar Ajandar Saidaita Nijeriya da mu ke magana, to dole ma’aikatar yaɗa labarai ce a sahun gaba.
“Wannan ma’aikata ce za ta kasance mai haska wa ƙasar nan fitilar kyakkyawar ɗabi’un jama’ar ta, kuma akwai wawakeken giɓi tsakanin gwamnati da jama’a, wanda wannan ma’aikatar ce tilas za ta iya cike giɓin,” inji sanatan.
“Na duba a cikin kasafin, amma ban ga ko sisi da za a kashe a Hukumar Kula da Jaridu ba, ban ga Hukumar APCON ba, kuma ban ga kasafin wasu hukumomin da ke ƙarƙashin wannan ma’aikata ba.
“Shin gwamnati na so ta shaida mana cewa an rushe waɗannan hukumomin kenan, yadda har za su iya aiki ko ba ma’aikata a cikin su?
“Wa zai biya albashin su? Watannin baya ba da daɗewa ba fa aka naɗa wa hukumomin sabbin Manyan Daraktoci da Manyan Sakatarori.
Kenneth ya ci gaba da cewa, “Mai Girma Minista, wannan batu ne fa mai muhimmanci ga wannan kwamiti, kuma tabbas za mu duba wannan lamari.”
A nasa bayanin, Minista Idris ya shaida wa sanatocin cewa za a ƙaddamar da Shirin Cusa Ɗa’a, Kishin Ƙasa da Kyawawan Ɗabi’u (NVC) cikin 2024.
Ya ce akwai gagarimin aiki a gaban ma’aikatar sa wajen tabbatar da samun nasarar shirin cusa ɗa’a da kishin ƙasa, wanda Naira biliyan 1 da aka ware wa ma’aikatar sa, a matsayin kuɗaɗen gudanar da manyan ayyuka, ko kusa ba za su wadata ba.