Mambobin Basij biyu sun rasu biyo bayan kai masu hari a Iran

Mambobi biyu na rundunar tsaro ta Basij da ke karkashin rundunar kare Juyin-juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) da ke Iran sun rasa rayukansu a ranar Asabar sakamakon hari da aka kai masu a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na Sistan-Baluchestan, kamar yadda yankin Kuds na rundunar ta IRGC ta bayyana a cikin wani jawabi.

“‘Yan ta’adda sun kai hari ga Hojatoleslam Sadegh Mahmoudi da Milad Damankesh a yayin da suke komawa gida daga wurin aiki a motar da take ba ta wurin aiki ba kuma sun yi shahada a yayin harin.” A cewar jawabin kamar yadda ya ke a rahoton kafar watsa labaru ta Iran International.

Su biyu din suna a wani bangare na shirin tsaro na Shahid Sajjad ne.

Kungiyar da ke dauke da makami ta Sunni, Jaish Al-Adl, a cikin wani jawabi a ranar Asabar ta dauki alhakin kai harin

Yankin Iran na Sistan-Baluchestan da dadewa dama yana fama da tashe-tashen hankula, inda Jaish Al-Adl ke kai masa hare-haren akai-akai, inda an san su ne da yin kwantan bauna, tayar da bama-bamai da hare-haren makamai da ya yi sanadiyyar rasuwar rayukan fararen hula da jami’an tsaro.

Al’amarin ya biyo bayan hauhawar tashe-tashen hankula ne a yankin. A watan Fabrairu, kungiyar ta dauki alhakin kai hari a Chabahar da ya lalata ofishin kula da al’amurra na gwamnati da kuma harin makami kan ginin wata gidauniya.

Jaish Al-Adl sun bayyana cewa wadannan hare-haren mayar da martani ne kan tsare-tsaren tayar da al’ummar Baluch na kauyuka.

Al’ummar Baluch suna daya daga cikin kabilun da suka fi talauci a Iran, inda suke shan wahala sakamakon rashin kayayyakin more rayuwa da gine-gine na kasa.

Iran da Amurka duka sun ayyana Jaish Al-Adl a matsayin kungiyar ta’addanci. Kungiyar ta kai hare-hare da dama a kan rundunar sojin Iran da wuraren da IRGC suke a ‘yan shekarun nan.

A cikin watan Nuwamba, mambobin rundunar IRGC hudu suka rasu a wata arangama yayin atisayen soja a yankin Rask. A watan Oktoba, Jaish Al-Adl ta dauki alhakin harin da ya yi sanadiyyar rasuwar sojojin Iran goma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *