Wani rahoto ya bayyana yadda manoman karkara a arewacin Nijeriya ke biyan har naira 100,000 ga ‘yan fashi da ‘yan ta’adda domin su kai ga gonarsu a lokacin shuka ko girbi.
Cikakken bayani a kan wannan na cikin wani rahoto ne na baya-bayan nan daga SB Morgen Intelligence, inda ya yi ikirarin cewa duk manomin da bai bi umarnin ba za a iya kashe shi, a sace shi ko a hana shi amfanin gonarsa.
Rahoton ya ce ‘yan fashi a wasu al’ummu a jihar Kaduna na tilastawa manoma biyan tsakanin naira 70,000 zuwa 100,000 domin a ba su izinin yin noma.
Rahoton ya ce, “A Kaduna, al’ummu a Kidandan, Galadimawa, Kerawa, Sabon Layi, Sabon Birni da Ruma abin ya shafe su sosai.
“Mazauna a wadannan yankuna sun ba da labarin biyan kudin da suka kai tsakanin naira 70,000 zuwa naira 100,000 domin samun izinin yin noma. Wadanda suka ki yarda da hakan kan fuskanci mummunan sakamakon da zai iya hadawa da sacewa, kashewa ko kwace amfanin gonarsu.”
Biyan kudin ga ‘yan fashi a jihar Zamfara ya danganta da hatsin da aka noma, inda manoma ke biya da yawa ga hatsin da ke da tsada. Kamar yadda binciken ya nuna, manoman shinkafa a wasu kananan hukumomi na biyan kusan naira 120,000 a matsayin harajin gona ga ‘yan fashi, inda masu noman dawa da masara a ke bukatar su biya naira 50,000 kawai.
Rahoton ya ma bayyana cewa biya ga ‘yan fashin za a iya yin sa da tsabar kudi ko da kudin da aka samu daga girbi, domin harajin ya fi yawa a lokacin girbi.
Rahoton ya ce ‘yan fashin su kan yi aikin da ke nuna bautar da mutane ta hanyar tilastawa ‘yan kauyen su samar tare da sayar da hatsi a garesu.
Tsakanin Nuwambar 2020 zuwa Nuwambar 2023, ‘yan fashi da ke ayyukansu a yankin jihohin arewa-maso-yammaci sun sa manoma sun biya harajin kusan naira miliyan 224.92. Da yawa da abin ya shafa an sace su, kuma a wasu lokutan, an kashe su, wanda hakan ke tilasta masu barin muhallansu.
Wannan mummunan yanayi shi ya ingiza mutanen karkara da dama suka bar noma, hakan kuma ya haifar da karancin kayan abinci a kasuwannin Nijeriya a fadin kasa.