Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima Ya Jagoranci Masu Tarbar Tsoho da Sabon Gwamnan Jihar Delta Zuwa APC

A wani Gangami na dubban jamaa,
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen tarbar gwamna Sheriff Francis Oborevwori na jihar Delta da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa da magoya bayansu wadanda suka yi ƙaura daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A jawabinsa na maraba, Shettima ya bayyana cewa daga yanzu, sabbin mambobin halatattun ‘ya’yan jam’iyyar APC ne, ba tubabbu ba, kana ya jaddada bukatar haɗin kai da aiki tare don tabbatar da muradin Jam’iyyar APC na kai ƙasar tudun-mun tsira. Inda Ya ce dama tattaunawa da mutunta ra’ayi na daga cikin sirrin wanzuwar Jam’iyyar ta APC

A nasa Jawabin, Gwamna Oborevwori ya bayyana cewa Jaharsa ba za ta iya cigaba da kasancewa a cikin ‘yan adawa da kyawawan manufofin Shugaba Tinubu na Fata Nagari ba, don haka suka yanke shawarar shigowa don a dama da su wajen gina wa Najeriya kyakkyawar makoma.

Shi ma Tsohon gwamnan jihar, kuma Mataimakin Dan Takarar shugaban kasa a Jam’iyyar PDP wanda ya dawo APC Ifeanyi Okowa, bayyana cewa ya dauki matakin komawa jam’iyyar APC ne don cimma muradun jiharsa da al’ummarta, sannan yayi alkawarin goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamna Oborevwori a zaɓe me zuwa

Taron gangamin ya samu halartar gwamnonin jihohi goma sha biyar da Sanatoci, da ma sauran manyan baki, wanda hakan ke nuna kafuwar wani babban tarihi a siyasar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *